Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar Za Ta Samar Wa Mali Dizal Domin Inganta Wutar Lantarki


Wutar lantarki
Wutar lantarki

Shugaban kasar Mali ya sanar a jiya Talata cewa, kasar Nijar za ta kai lita miliyan 150 na dizal domin samar da wutar lantarki a makwabciyar kasa ta Mali a daidai lokacin da kasar ta yammacin Afirka ke fama da matsalar rashin wutar lantarki.

Kimanin mutane miliyan 11, ko kuma kusan rabin al'ummar Mali, ke samun wutar lantarki a kasar, wadda shugabannin sojoji ke mulkita tun bayan juyin mulkin shekarar 2020.

Amma kamfanin makamashi na kasa (EDM-SA) ya na durkushewa sanadiyyar bashin sama da biliyan 200 na CFA, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 330 kuma ya kasa tabbatar da ci gaba da samar da wutar lantarki a Bamako babban birnin kasar da sauran garuruwan Mali.

Shugaban mulkin sojan Mali, Kanar Assimi Goita, a ranar Talata ya gana da ministan man fetur na Nijar, Mahaman Moustapha Barke, don kammala "yarjejeniya ta hadin gwiwa ta sayar da litar man dizal miliyan 150 ga Mali," in ji fadar shugaban kasar Mali a cikin wata sanarwa.

Assimi Goita
Assimi Goita

A cikin sanarwar, Barke ya ce "Wannan man fetur din zai isa kamfanin Energie du Mali (EDM-SA) don samar da tashoshin wutar lantarki na kasar."

A cikin watan Fabrairu ne Nijar ta sanar da rattaba hannu kan yarjejeniyar samar da dizal ga Burkina Faso, Mali da Chadi, kasashen da suka fi talauci a duniya da kuma gwamnatocin soja.

Kasashen Nijar da Burkina Faso da Mali sun hada kai don kafa kawancen kasashen yankin Sahel (AES), kuma a cikin watan Fabrairu sun sanar da ficewarsu daga kungiyar ECOWAS ta yammacin Afirka.

A cikin watan Nuwamba ne hukumomin Nijar suka kaddamar da wani katafaren bututun mai da zai dauko danyen mai da aka hako daga yankin kudu maso gabashin Agadem zuwa makwabciyar kasa ta Benin.

Kamfanin (CNPC) mallakar gwamnatin kasar China ne ke hako man.

Hukumomi a Nijar sun ce a ranar 13 ga watan Afrilu sun samu lamuni na dala miliyan 400 daga abokan huldarsu na kasar China a matsayin wani ci gaba kan cinikin danyen mai da ke tafe, wanda za a fara sayar da shi a watan Mayu.

Kasar na shirin kara yawan man da take hakowa zuwa ganga 110,000 a kowace rana, inda za a rika fitar da ganga 90,000 zuwa kasashen waje.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG