Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tituna Da Filin Jirgin Saman Dubai Sun Malale Da Ruwa Bayan Da Aka Yi Wani Ruwan Sama Da Ba A Saba Yi Ba


Ambaliyar ruwa ta rufe manyan titunan birnin Dubai
Ambaliyar ruwa ta rufe manyan titunan birnin Dubai

Ambaliyar ruwa ta rufe manyan titunan birnin Dubai kuma babban filin jirgin samansa ya kasance cikin rudu yayin da cibiyar hada-hadar kudi ta Gabas ta Tsakiya din ta kasance a kulle a ranar Laraba, kwana guda bayan da aka yi ruwan sama mai tsananin gaske da ba a taba irinsa ba.

A kalla mutum daya ya mutu, wani dattijo mai shekaru 70 da haifuwa, a cikin motarsa a Ras Al-Khaimah, daya daga cikin masarautun kasar bakwai masu arzikin man fetur, in ji ‘yan sanda.

An samu katsewar wutar lantarki a kusa da birnin Dubai, wanda ke cike da ambaliyar ruwa da ya nitsar da motocin da aka bari.

UAE-BAHRAIN-OMAN-WEATHER-FLOOD
UAE-BAHRAIN-OMAN-WEATHER-FLOOD

An ga irin wannan al'amuran a kusa da yankunan da suka hada da Sharjah, makwabciyar Dubai, inda mazauna yankin suka yi ta ratsa manyan tituna tare da kai komo a cikin kwale-kwale na wucin gadi.

"Wannan shi ne lamari mafi muni da na taba fuskanta," in ji wani dan kasar Dubai mai shekaru 30, wanda ya so a sakaya sunansa, bayan wata tafiyar tsawon mintuna 15, ya koma sa'o'i 12 a kan tituna da ambaliyar ruwa ta mamaye."

UAE-BAHRAIN-OMAN-WEATHER-FLOOD
UAE-BAHRAIN-OMAN-WEATHER-FLOOD

"Na san cewa idan motata ta lalace zata nutse ni ma kuma zan nutse da ita."

Makarantu za su ci gaba da kasancewa a rufe a Dubai har zuwa mako mai zuwa, in ji hukumomi, wanda ke nuna irin wahalar tsaftace muhallin.

A halin da ake ciki, ayyuka suna yi tafiyar hawainiya a filin jirgin sama na Dubai, mai tasha mafi yawan zirga-zirgar jiragen sama a duniya, yayin da ma'aikatan suka kasa isowa aiki sakamakon ambaliyar ruwa, sannan kuma aka dakatar da akasarin motocin zirga-zirgar jama'a.

Arabian Peninsula Rain
Arabian Peninsula Rain

Yayin da aka jinkirta kusan kowane jirgi akai-akai, an gaya wa fasinjoji su nisanci filin "sai dai idan ya zama dole," in ji ma’aikatan Filin jirgin saman Dubai.

An kuma jinkirta tashin jirage da dama, an soke da kuma karkatar da su a lokacin da aka yi ruwan sama kamar da bakin kwarya a ranar Talata, lokacin da jiragen suka ce su na yunkurin tashi cikin ruwa mai zurfi.

Guguwar ta afka wa kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain ne da daren jiya litinin da kuma ranar Talata bayan da a baya suka afka wa kasar Oman, inda mutane 19 suka mutu ciki har da kananan yara.

Maryam Al Shehhi, babbar jami’ar hasashen yanayi a cibiyar nazarin yanayi ta UAE, ta musanta rahoton da ke cewa Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi shukar gajimare inda ta fesa sinadarai don kara yawan ruwan sama.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG