Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Burkina Faso Sun Kori Jami'an Diflomasiyyar Faransa 3


Wasu sojoji da suke fice daga Nijar
Wasu sojoji da suke fice daga Nijar

Gwamnatin mulkin soji a Burkina Faso ta kori wasu jami'an diflomasiyyar Faransa uku bisa zarginsu da yin zagon kasa, kamar yadda wata takarda da gwamnati ta wallafa a shafukan sada zumunta ta ce  ranar Alhamis.

Majalisar mulkin sojan kasar ta bayyana sunayen jami’an diflomasiyyar guda uku, wadanda biyu daga cikinsu masu ba da shawara ne kan harkokin siyasa, ta kuma ayyana su a matsayin wadanda ba a gayyace su ba a Burkina Faso, a cewar takardar da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta sanya wa hannu tun a ranar Talata. An ba su sa’a 48 su bar Burkina Faso.

Takardar ba ta ba da cikakken bayani ba game da ayyukan zagon kasa da ake zargin su da aikatawa.

Ma'aikatar harkokin wajen Faransa a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, ta ce ta yi nadamar matakin korar jami'an diflomasiyyarta tare da yin watsi da zarge-zargen, tana mai cewa ayyukanta a Burkina Faso na cikin tsarin huldar jakadanci da na ofishin jakadancin Majalisar Dinkin Duniya.

Sanarwar ta ce "shawarar da mahukuntan Burkina Faso suka babu wata takamaimiyar hujja." "Mun dai yi bakin cikin lamarin."

Korar ta zo ne a daidai lokacin da dangantaka ta tabarbare tsakanin Burkina Faso da Faransa wacce ta yi wa kasar mulkin mallaka.

Gwamnatin mulkin soja ta yanke huldar soji da Faransa a shekarar 2023, inda ta umurci daruruwan sojojin Faransa da su fice daga yammacin Afirka cikin wata guda, bisa tafarkin makwabciyarta Mali, wadda ita take karkashin jagororin juyin mulki.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG