Wani kwale-kwalen kamun kifi ya nutse a kogin Zambezi da ke tsakiyar kasar Mozambique, inda ya kashe mutane takwas da suka hada da yara shida.
Kifewar kwale-kwalen ta ranar Litinin a lardin Sofala na zuwa ne mako guda bayan wani hatsarin jirgin ruwa ya halaka mutane kusan 100, yawancinsu kananan yara, a tazarar kimanin kilomita 1,000 (mil 600) zuwa arewa.
Hukumomin gundumar Caia sun shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, kwale-kwalen na dauke da mutane 12 galibi manoma.
Mutane biyu ne suka tsira da ransu, wasu biyu kuma ba a gansu ba. Yara shida na cikin wadanda suka mutu.
Hukumomi sun ce ana ci gaba da neman wadanda suka bace.
A ranar 7 ga watan Afrilu, wani jirgin ruwa dauke da kaya ya kife ya kashe mutane 98. Jirgin na dauke da iyalai da dama da suka firgita yayin da su ke kokarin tserewa barkewar cutar kwalara.
Dandalin Mu Tattauna