Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Senegal Ta Kama Tan Guda Na Hodar Ibilis


Hodar iblis
Hodar iblis

Hukumar Kwastam ta Senegal ta ce ta kwato fiye da tan guda na hodar ibilis a kudu maso gabashin kasar, inda ta bayyana shi a matsayin kamu mafi girma da aka taba yi na jigilar hodar iblis a kan hanyar kasa a yammacin Afirka.

Hukumar Kwastam ta ce an kama hodar ibilis mai nauyin kilogiram 1137.6 a ranar Lahadin da ta gabata a garin Kidira, wacce ta kiyasta kudinsa zai kai sama da CFA biliyan 90, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 146.

Sanarwar ta ce, wannan shi ne kamu mafi girma na hodar iblis ta hanyar kasa da aka taba samu a Senegal.

hodar iblis
hodar iblis

An boye hodar ne a cikin fakiti-fakiti kuma “an sanya shi a cikin jakunkuna a cikin kasar wata mota mai daukar kayan sanyi da ta fito daga wata kasa mai makwabtaka da Senegal,” in ji ta, ba tare da bayyana sunan kasar ba.

Hukumar kwastam ba ta ce uffan ba da AFP ya nemi karin haske kan lamarin.

Kasar Senegal dai tana iyaka da kasashen Guinea da Gambia da Guinea Bissau da Mauritania da kuma Mali, kasashen da aka san su ne wuraren safarar magungunan da ake samarwa a Amurka ta Kudu akan hanyarsu ta zuwa Turai.

Yammaci da tsakiyar Afirka ya zama yankin da ake yawan amfani da shi, a cewar ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai yaki da miyagun kwayoyi da laifuffuka.

A watan Oktoban 2022, an kama kilogiram 300 na hodar iblis daga wata motar daukar kaya mai sanyi da ta taho daga Mali.

Rundunar sojin Senegal a watan Nuwamban da ya gabata ta ce ta gano kusan tan uku na hodar iblis daga wani jirgin ruwa a gabar teku.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG