Da farko dai 'yan ta'addan sun nuna turjiya, amma biyo bayan barin wuta ba kakkautawa, ala tilas ba girma ba arziki suka saduda.
Wani dattijo kuma Shugaban Majalisar Koli ta Shari'a a Najeriya (SCSN), Dr Datti Ibrahim Ahmed, ya rasu.
Gwamnatin jihar Katsina ta bukaci al’ummar jihar da su yi duk abin da ya dace ciki har da addu’a ko ma samun makamai domin kare kansu daga ‘yan bindiga da suka addabi jihar.
Mutane uku ‘yan gida daya na daga cikin mutum bakwai da suka mutu a wani hatsarin jirgin ruwa a kauyen Zhigiri da ke karamar hukumar Shiroro a jihar Nejar Najeriya.
A yayin da ake ci gaba da neman bakin zare don warware matsalolin tsaro musamman a arewacin Najeriya, masu fada a ji sun bayyana cewa komawa kan tarbiyya ta kwarai zai taimaka wajen kawo karshen miyagun iri a kasar.
Kungiyar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje, Turai (NIDO-Europe), reshen Italiya, ta ce kimanin mutane miliyan 1.5 daga cikin miliyan 3 da suka yi wa rajista a Italiya na fama da karancin fasfo na Najeriya.
Likitoci a Isra'ila sun fara ba da kashi na hudu na rigakafin mai kara kuzari na COVID-19 a ranar Litinin a zaman wani bangare na binciken gwaji don tantance ko karin harbin na iya bunkasa karfin rigakafi daga cutar.
Wasu gawarwakin bakin haure 28 sun bullo a gabar tekun yammacin kasar Libya bayan da kwale-kwalen da suke ciki ya nutse a ranar Lahadi, lamarin da ya kasance mafi muni na baya-bayan nan kan hanyar hijira mai yawan hatsari na duniya.
Babban mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama'a, Garba Shehu ya kamu da cutar coronavirus kuma yana kan jinya.
Karuwar yaduwar cutar coronavirus ya sa kasashen larabawa sun dakatar da Najeriya da sauran wasu kasashen Afirka zuwa kasashensu.
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya taya Kristoci murnar bikin Kirsimeti da tare da fatan shiga sabuwar shekara lafiya.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da bayar da iyakacin kokarinta na ci gaban kasar har zuwa watan Mayu, 2023, yana mai jaddada cewa zai mika mulki kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.
A karo na uku a jere cikin wannan mako 'yan-bindiga sun sake tare hanyar Kaduna-zuwa Birnin Gwari inda su ka datse ayarin motoci masu rakiyar jami'an tsaro, su ka kashe mutane sannan su ka sace wasu da dama.
‘Yan bindiga sun kai tagwayen hare-hare a wasu tashoshin bincike a garin Makalondi dake jihar Tilabery iyaka da Burkina Faso inda suka hallaka jami’an tsaro tare da kona motoci sannan suka arce da wasu motocin ‘yan sanda.
Kungiyar daliban arewa masu karatun digiri na daya zuwa na uku a kasar Burtaniyya sun gudanar da zanga-zangar lumana don mika kokensu a game da yanayin tabarbarewan tsaro a arewacin kasar.
Yanzu Majalisar ta cewa ba za a taba dokar ba sai bayan an dawo daga hutun karshen shekara a ranan 18 ga watan Janairun shekara 2022.
Najeriya ta lalata alluran rigakafin cutar COVID-19 sama da miliyan 1 na AstraZeneca a ranar bayan da hukumomi suka ce ba za a iya amfani da su ba kafin ranar karewar su.
Bisa al’ada akan ba ma’aikatan fadar shugaban kasa da na gwamnati hutu a lokacin bukukuwa daban-daban, amma ba kasafai ake ba su umarnin su zauna a gida har sai an neme su ba.
Makonni kalilan bayan bullar sabon nau’in cutar Corona da ake yiwa lakabi da Omicron, gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da shirin allurar rigakafi na bai-daya a fadin jihar, sai dai wasu daga al’ummar jihar na nuna rashin sha’awarsu ga allurar.
A Najeriya ‘yan bindiga na ci gaba tayar da hankalin jama'a ta hanyar hare-haren ta'addanci musamman a arewa maso yammacin kasar.
Domin Kari