Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gano Gawarwakin Bakin Haure 28 A Gabar Tekun Libya


Wasu gawarwakin bakin haure 28 sun bullo a gabar tekun yammacin kasar Libya bayan da kwale-kwalen da suke ciki ya nutse a ranar Lahadi, lamarin da ya kasance mafi muni na baya-bayan nan kan hanyar hijira mai yawan hatsari na duniya.

Tawagar kungiyar agaji ta Red Crescent ta Libya sun gano gawarwakin bakin haure 28 da suka mutu, inda suka gano wasu mutane uku da suka tsira a wurare daban-daban guda biyu a gabar tekun Al-Alous, mai tazarar kilomita 90 daga birnin Tripoli.

“Yanayin rubewar gawarwakin na nuni da cewa jirgin ya kife ne kwanaki da dama da suka gabata,” in ji shi, inda ya kara da cewa adadin na iya karuwa cikin sa’o’i masu zuwa. Hotunan da kafafen yada labaran Libya suka wallafa sun nuna gawarwakin da aka yi layi da su a bakin tekun sannan aka sanya su cikin ledojin matattu.

Libya, wacce ta kwashe shekaru goma tana fama da rikice-rikice da rashin bin doka da oda, ta zama babbar hanyar tashi ga bakin haure daga Afirka da Asiya da ke kokarin shiga Turai.

Galibin bakin haure suna jure munanan yanayi yayin da suke Libya kafin su kama hanyar bulaguro zuwa arewa cikin cunkoso, kuma galibi cikin jiragen ruwa da ke nutsewa ko shiga cikin matsala.

Wannan sabon bala'i ya zo ne kwanaki kadan bayan da bakin haure 160 suka mutu a cikin mako guda a irin wannan lamari, wanda ya kawo adadin rayukan da suka mutu a bana zuwa 1,500 a cewar hukumar kula da 'yan cirani ta duniya.

Hukumar ta IOM ta ce an kama bakin haure sama da 30,000 a lokaci guda aka kuma dawo da su Libya.

Kungiyar Tarayyar Turai ta hada kai da jami'an tsaron gabar tekun Libiya domin rage yawan bakin haure da ke isa gabar tekun Turai. A lokacin da aka dawo su, da dama na kara fuskantar karin munanan cin zarafi a wuraren da ake tsare da su.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG