Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Komawa Zamantakewa Irin Ta Da Ce Maslaha Ga Matsalar Tsaron Najeriya - Masu Fashin Baki


Wasu daga cikin sarakunan gargajiya a Arewacin Najeriya (Facebook/Gwamnatin Filato)
Wasu daga cikin sarakunan gargajiya a Arewacin Najeriya (Facebook/Gwamnatin Filato)

A yayin da ake ci gaba da neman bakin zare don warware matsalolin tsaro musamman a arewacin Najeriya, masu fada a ji sun bayyana cewa komawa kan tarbiyya ta kwarai zai taimaka wajen kawo karshen miyagun iri a kasar.

A kusan kullum magana daya ke ci gaba da ci wa al’umman arewacin Najeriya tuwo a kwarya sakamakon yadda ‘yan bindiga ke kashe-kashen al’ummomin da ba su ji ba su gani ba.

Hakan ya kai ga kiraye-kirayen gwamnati kawo karshen matsalolin na tsaro daga matasa, dattawa, sarakunan gargajiya, malamai da ma sauran al’umma.

Sarkin Jiwa, Dakta Idris Musa, ya bayyana cewa kamata ya yi al’umma ta duba batun tarbiyyar daga sama zuwa kasa don samun mafita mai dorewa.

Tuni dai matasan arewacin Najeriya a kafaffen sada zumunta suka fara gangamin neman gwamnatin Najeriya ta sake salo a yakin da take da 'yan ta’adda don samawa mutanen yankin tsaron da su ke bukata na gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum.

Kona fasinjoji da 'yan bindiga suka yi na kwanakin baya-bayan nan a jihar Sokoto da kuma kisan wasu talakawa 43 da aka yi a yankin Giwa da ke jihar Kaduna na daga cikin ayyukan bata-gari da ya sa 'yan arewacin kasar ke cewa tura ta kai bango.

Sai dai gwamnati na dada jaddada cewa tana iya bakin kokarinta wajen shawo kan matsalolin tsaron.

Saurari cikakken rahoton a cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00


XS
SM
MD
LG