Karuwar yaduwar curtar coronavirus da rashin sanin tabbas game da tsarin tattara bayanan Najeriya, lamarin da ya sa Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta hana matafiya daga kasashen Najeriya da Kenya da Tanzania da kuma Habasha kasashen Daular, don tabbatar da cewa masu dauke da kwayar cutar ba za su shiga cikin kasarsu ba.
Rahotanni sun nuna cewa hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa (NCEMA) da hukumar kula da fufurin jiragen sama ta kasa (GCAA) sun sanar da dakatar da dukkan zirga-zirgar jiragen sama na masu jigilar kayayyaki na kasa da kasa da kuma masu jigilar fasinjoji daga kasashen hudu daga ranar Asabar 25 ga watan Disamba.
Wani bangare na sabuwar dokar ta COVID-19 da UAE ta gabatar ya hada da dakatar da shigar matafiya da ke cikin kasashen hudu kwanaki 14 kafin su zo UAE.
Hukumomin sun bayyana cewa sassan da aka ware ya kamata su gabatar da gwajin COVID-19 da ya nuna basu kamu da cutar ba cikin awanni 48, kafin tashin jirgi sai an yi gwajin coronavirus na PCR a filin jirgin sama cikin sa'o'i shida kafin ya tashi da kuma gwajin PCR a filin jirgin sama lokacin isa UAE.
GCAA ta kuma bayyana cewa ana bukatar wadanda suka fito daga kasashen hudu da suka biyo ta wasu kasashe su zauna a kasashen na akalla kwanaki 14 kafin a basu izinin shiga UAE.
Har ila yau, an hana 'yan hadaddiyar daular larabawa yin balaguro zuwa ƙasashen Afirka huɗu ban da lamurra na gaggawa na ƙasar, ko wakilai na hukuma ko tallafin karatu.
Bugu da kari, hukumomin biyu sun gabatar da sabbin sharuddan balaguro ga wadanda ke zuwa daga Uganda da Ghana.
Da yake mayar da martani kan sabuwar dokar COVID-19 ta UAE, tsohon shugaban hukumar kula da balaguro ta Najeriya (NANTA) da Manajan Darakta kuma Shugaba na Kamfanin Finchglow Group, Bankole Bernard, ya ce watakila an saka Najeriya a cikin jerin sunayen saboda ba ta da ingantaccen tsarin takaddun bayanai kan masu kamuwa da COVID-19 musamman tsakanin matafiya.
“Daya daga cikin abubuwan da ya kamata mu fahimta shi ne, COVID-19 ta zama kayan aiki na siyasa da tattalin arziki, wanda kasashe ke amfani da su don cimma muradunsu a cikin hadin gwiwar kasashe, musamman a fannin tafiya ta jirgin sama. Idan kun lura da yaduwar wannan nau'in na Omicron, yana da sauri sosai. Ba mutuwa bace, amma ta na shafar mutane da yawa kuma ana samun sakamako na karya da yawa da ke fitowa a cikin kasarmu. Ba za su iya dogara da bayananmu ba. Ba mu san yadda ake adana bayanan ba, ”in ji shi.