Majalisar Dokokin Najeriya ba ta kai ga cimma matsaya kan makomar kudurin dokar zabe da shugaba Muhammadu Buhari ya ki rattaba hannu akai.
A farkon makon nan shugaban na Najeriya ya ki rattaba hannu akan dokar yana mai cewa tsarin ‘yar tinke da dokar ta zaba zai iya haifar da rudani sannan za a kashe makudan kudaden wajen gudanar da shi.
Hakan ya sa wasu ‘yan Majalisar Dattawa 80 suka wallafa sunayensu a matsayin wadanda suke so a bijire wa matakin da shugaba Mohammadu Buhari ya dauka na kin sa hannu akan sabuwar dokar zaben.
Amma daga wani bangare, kwatsam, sai ga sanarwa da ke nuna akasin bijire wa daga bakin Shugaban Majalisar dattawa Ahmed Lawan.
Majalisun biyu sun dauki matakin ajiye dokar bayan shugaba Mohammadu Buhari ya mayar masu da ita a bisa hujjar ba zai sa hannu ba.
Daga wannan gabar, alamu suka fara nuna cewa da sauran rina a kaba akan dokar zaben da manyan ‘yan siyasa, kungiyoyi masu zaman kansu da masu ruwa da tsaki a kasar suka riga suka yaba da ita.
A Majalisar dattawa an kwashi lokaci ana tara sunayen Sanatoci da suka amince majalisar ta bijire wa Shugaban kasa, ta yi gaban kanta ta nuna karfin ikon da Kundin tsarin mulki ya tanadar mata, ta sa hannu a dokar zaben.
Amma bayan da suka rufe kofa har sau biyu, sai kawai Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan ya fara jawabi mai nuna goyon baya ga matakin da Shugaban kasa ya dauka, da kuma matsayin Majalisar na cewa ba za a taba dokar ba sai bayan Majalisa ta dawo daga hutun karshen shekara a ranan 18 ga watan Janairu na shekara 2022.
Saurari cikakken rahoton Medina Dauda daga Abuja: