Shugaban Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Najeriya Faisal Shuaib, ya ce jami’an kiwon lafiya a kasar da ta fi kowacce yawan jama’a a Afirka, ba ta da wata dabara illa su dauki wannan matakin bayan sun karbi gudummawar alluran rigakafin da ba su da sauran rai.
"Akwai kasashe da suka ci gaba da makon waddanan alluran rigakafin," in ji shi. "A lokacin da ranar amfaninsu ke gab da ƙarewa, sai suka ba da su gudummawa."
A makon da ya gabata Shu’aib ya sanar da cewa Najeriya ba za ta sake karbar irin wadannan gudummarwa ba.
Kashi 2 cikin 100 na al'ummar Najeriya miliyan 206 ne kawai ke da cikakkiyar rigakafin, kuma jami'an kiwon lafiya sun kafa wani gagarumin buri na yin allurar fiye da kashi daya bisa hudu na al'ummar kasar nan da watan Fabrairu. Yayin da shakku ya yi yawa, adadin rigakafin kasar ya kusan ninki biyu a cikin makon da ya gabata.
Najeriya na ta ganin karuwar masu kamuwa da cutar tun bayan da ta gano nau'in omicron mai saurin yaduwa a karshen watan Nuwamba, wanda ya samu karuwar kashi 500% a cikin makonni biyu da suka gabata, a cewar Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya.
A ranar Talata an tabbatar da sabbin masu cutar 2,123 a matsayin shine mafi girman adadin yau da kullun tun daga watan Janairun da ya gabata kuma na biyu mafi girma tun bayan barkewar cutar.
"Idan za mu shawo kan wannan cutar ta COVID-19, dole ne mu yi aiki mai kyau na tabbatar da samar da ingantacciyar rigakafin COVID-19," in ji Shuaib. "Babu wata kasa da za ta iya kawar da COVID-19 har sai duk kasashen sun sami damar kawar da shi."