Majalisar limaman Islama ta yankin Sahel a Afirka wato Rabidatul Islam Fi Biladi Sahel ta kammala taro kan lamuran tsaro a Abuja, babban birnin Najeriya da ganawa ta musamman da kungiyar JIBWIS.
Gwamnatin jihar Jigawa da hadin gwiwa da Ofishin Majalisar dinkin duniya mai kula da manyan laifuka da ta’ammali da miyagun kwayoyi za su kafa hukumar yaki da rashawa da karbar korafe-korafen Jama’a a jihar wadda ake sa ran za ta fara aiki a cikin sabuwar shekara.
Kungiyar Fulani ta Walidra da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Najeriya ta koya wa mata fulani 200 sana'o'i hannu a Rugan Julie da ke karamar hukumar Karu ta Jihar Nasarawa domin taimaka masu su samu dogaro da kansu daga mawuyacin halin da yan bindiga suka jefa yawancin su a ciki.
A Najeriya alamu na nuna akwai yuwuwar an soma fafatawa don dakile ayukkan ‘yan bindiga a wasu yankunan arewacin Najeriya domin mazauna yankunan sun tabbatar da ganin jami'an soji suna dannawa zuwa inda ake tunanin mafakar ‘yan bindigar ce.
Gamaiyyar Kungiyoyin Kwadago a Najeriya ta ce za ta yi iya kokarin ta wajen ganin ba a kara kudin man fetur ba.
Yayin da ake ci gaba da samun tabarbarewar tsaro, gwamnatin jihar Neja ta tabbatar da karbar harajin da ‘yan bindiga ke yi a jihar kamar yadda wasu majiyoyin suka rawaito.
A Jamhuriyar Nijar shugabanin al’umar karkarar Lahari dake yankin Diffa sun bayyana damuwa dangane da yanayin da ayyukan hakar man fetur suka jefa su ciki inda gurbacewar muhalli ta shafi ayyukan noma da kiwo.
Masu ruwa da tsaki a fannoni daban-daban na Najeriya sun kwashe kwanaki biyu suna tattauna makomar kasar a Abuja.
A ranar Laraba ne majalisar dattawan Najeriya ta amince da bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari na karbo bashin dala biliyan 5.8 daga kasashe masu ba da lamuni na duniya.
A Najeriya bisa ga yadda matsalolin rashin tsaro ke ci gaba da wanzuwa, duk da kokarin da ake yi na magance su, ‘yan kasar sun soma tunanin cewa ya kamata gwamnati ta kirkiro runduna ta musamman daga cikin jama'ar yankunan da ke fama da matsalolin su kare yankunan su.
A Najeriya gwamnonin kasar sun sha alwashin jajircewa ta kowace hanya za'a samu saukin matsalolin rashin tsaro, zasu bi ta don ganin an samu shawo kan matsalolin.
Hukumomin New Zealand na binciken wani mutum da aka yi wa allurar rigakafin Covid-19 har sau 10 a rana guda.
Gwamnatin mai girma Muhammadu Buhari ta kan aika mutane a je a yi wa jama’a jaje a nuna rashin jin dadi kuma a yi musu tabbacin cewa an kawo karshen wannan al’amarin.” In ji Monguno.
Jami’an tsaro sun kama kusoshin wata kungiyar fafutika cikinsu har da wani dan kasar Faransa.
La’akari da yanda arewacin Najeriya ke cikin halin ha’ula’i sakamokon cigaba da tabarbarewar tsaro da yankin ke fuskanta musamman a cikin sati biyu da suka gabata, mata masu fafatuka sun ce kowa ya kare kansa.
Tirka tirkar da ta faru har aka rasa wuta a babban birnin tarrayya da wasu Jihohi 5 a kwanakin baya ya fusatar da Kwamitin Kula da Bangaren Wutar Lantarki ta Majalisar Wakilai.
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wani kauye a arewacin Najeriya, inda suka kashe masu ibada akalla 16 a wani masallaci tare da yin garkuwa da wasu, in ji wani jami’in yankin.
A ranar Juma’a ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike da wata babbar tawaga wadda ta kunshi shugabannin hukumomin leken asiri da tsaro na kasa zuwa jihohin Sokoto da Katsina domin mayar da martani kan yawaitar ayyukan ‘yan fashi da makami.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Sanusi Buba, ya tabbatar da rasuwar kwamishinan da daren jiya Alhamis yayin da yake zantawa da manema labarai a gidan marigayin da ke gidajen estate din Fatima Shema kamar yadda wasu majiyoyi suka rawaito.
Majalisar Dattawan Najeriya na shirin kafa wata hukuma da za ta rika kula da bayanai ta kasa, wadda za ta daidaita ayukan hukumomi da suka dace.
Domin Kari