An kama sama da kilogiram 22,160 na maganin kodin da kwayoyin methamphetamine da kuma tabar wiwi a tashar ruwa ta Apapa da kuma wani katafaren gidan kwayoyi mai suna Akala da ke Mushin a Legas.
A yayin da zanga-zangar adawa da matakan kiwon lafiya na gwamnatin Canada da umarnin alluran rigakafi suka shiga rana ta goma sha ɗaya yau Litinin, 'yan sanda sun yi barazanar yin tattaki bayan da suka fuskanci suka kan rashin daukar matakin da ya gurgunta babban birnin ƙasar.
Akalla mayakan kungiyar ISWAP 104 na lardin Yammacin Afirka, sun mika wuya ga sojojin Najeriya a jihar Borno.
A ci gaba da bikin ranar Hijabi ta duniya, mata da ‘yan mata a jahar Filato sun jaddada muhimmancin sanya Hijabi ga mace, don kare mutuncinta, da na addininta, da rage cin zarafin mata da ke yawaita.
Sakamakon hauhawar farashin man fetur, Najeriya na daukar matakan dakile satar mai, a wani bangare na kokarin da kasar ke yi na maido da kudaden da ta yi asarar su.
Kamfanin harhada magunguna na Afirka ta Kudu Afrigen shi ne na farko a nahiyar da ya fara kirkiro rigakafin mRNA na COVID-19 ta hanyar amfani da bayanan hada magani na kamfanin Moderna. Kamfanin na fatan fara gwajin maganin rigakafin a watan Nuwamba.
Daruruwan mutane da 'yan bindiga suka tarwatsa daga garuruwansu suka cika sansanin 'yan gudun hijira na garin Gwada ta yankin karamar hukumar Shiroro a jihar Nejan Najeriya.
Shugaban kungiyar ECOWAS na yammacin Afirka ya ce dole ne a shawo kan juyin mulkin da aka yi tun bayan juyin mulkin gwamnatin sojan kasar Mali a shekarar 2020 kafin ta lalata yankin baki daya.
Wani jirgin dako da hakon mai ya fashe a kudancin jihar Delta kuma ana fargabar ma'aikatan jirgin 10 sun mutu, in ji hukumomin Najeriya.
Kwamitin sulhu na 'ya'yan jam'iyyar APC da su ka samu sabani sanadiyyar zabukan gundumomi, kananan hukumomi da jihohi, ya bar baya da kura bayan mika rahotonsa ga shugabanin rikon jam'iyyar.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, da yammacin ranar Talata, ya zanta da Umaro Sissoco Embalo, jim kadan bayan shugaban na kasar Guinea Bissau ya tsallake rijiya da baya a yunkurin da sojoji suka yi na hambarar da gwamnatinsa.
Shugaba Buhari ya yi wannan alkawarin ne ranar Talata a Abuja yayin da ya karbi bakuncin mambobin kungiyar addinai ta Najeriya NIREC.
Gwamnatin jihar Kaduna ta ce an kashe mutane 1,129) a fadin jihar Kaduna a bara, sannan an kiyasta cewa kullum akan sace mutane tara a fadin jihar.
Gwamnatin jihar Filato ta ce ta bullo da wani sabon tsari na fadakar da al’umma kan su sanya ido kan makwabtansu, don gano wadanda ke fakewa suna kashe mutane da yin garkuwa da su.
Al’ummar Erei dai sun shafe shekaru suna takun saka a kan wani fili da rusassun yankin Gabashin kasar ya kafa kafin yakin basasar Najeriya a matsayin matsugunin na gonar ‘ya’yan manja.
Sakataren gwamnatin jihar Nejan Alh. Ahmed Ibrahim Matane ya ce ba su da labari kan lamarin makafin.
Samun wannan galaba na zuwa ne a daidai lokacin da talakawa a wasu kasashen yankin Sahel ke zargin mahukunta da gazawa a fannin samar da tsaro.
Rahotanni daga jihar Nejan Najeriya na nuna cewa wasu 'yan bindiga sun kai harin da ya hallaka akalla mutum 8 tare da yin garkuwa da wasu da dama a jihar.
Wasu al'umomin garuruwa 11 dake karamar hukumar Birnin Gwari, a jihar Kaduna, sun ce sun hada sama da naira miliyan 30 a matsayin kudin neman sasantawa da 'yan bindiga.
Fadar shugaban kasar Nijar ta maida martani akan wata jita jitar dake cewa shugaba Mohamed Bazoum ya daina kwana a fadarsa tun ranar da sojoji suka yi juyin mulki a Burkina Faso.
Domin Kari