A yayin bude taron kungiyar ECOWAS karo na biyu kan batun juyin mulkin da aka yi a watan Janairu a Burkina Faso, shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo, ya ce sake aukuwar juyin mulki a yammacin Afirka abin damuwa ne, kuma dole ne a dakile shi.
Akufo-Addo ya ce, "da ajiyar zuciya ne na ke yi muku maraba a yau zuwa Accra bayan ganawar da muka yi a makon jiya ta yanar gizo." "Kasancewar ku a nan wata alama ce mai karfi da ke nuna aniyarku na ganin an samar da mafita mai ɗorewa ga sake aukuwar fitinar a yankinmu.
Ya kamata mu magance wannan al'amari mai haɗari kafin ya lalata yankin baki ɗaya."
A cikin shekarar da ta gabata, an yi jerin juyin mulki da kuma yunkurin juyin mulki a kasashen Yammacin na Afirka da suka hada da Burkina Faso, Chadi, Guinea da kuma Guinea-Bissau.
Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika ta dakatar da kasashen Burkina Faso, Guinea da Mali daga kungiyar mai mambobi 15 tare da kakaba takunkumi kan kasashen Guinea da Mali bayan da sojoji suka mamaye iko. Kungiyar Tarayyar Afirka ta kuma dakatar da kasashen uku.
To sai dai masana na tambayar shin ko takunkumin yana da tasiri ne a lokacin da ake gudanar da juyin mulkin saboda damuwar da jama'a ke da shi game da tsaro da kuma yaki da kungiyoyin IS da masu alaka al-Qaida.
Shugaban kwamandan rundunar sojin Ghana da kwalejin ma’aikata (Dean of the Ghana Armed Forces Command and Staff College), Vladimir Antwi-Danso ya shaidawa Muryar Amurka cewa dole ne kungiyar ECOWAS ta kara zage damtse wajen taimakawa kasashe mambobin kungiyar don magance matsalar tsaro.
“Karni na 21 karni ne na ta’addanci,” in ji shi. "Abin yana kara ta'azzara. Kuma abin da ya kamata mu kara maida hankali akai ke nan maimakon kungiyoyin AU da ECOWAS su yi ta Allah wadai da juyin mulki da rufe iyakokin.
Tsohon darektan hukumar kula da tattalin arzikin Afirka ta Majalisar Dinkin Duniya Takyiwaa Manuh ya fi sukar kungiyoyin kasashen Afirka. Da yake magana a gidan rediyon Asaase na Ghana, ya ce ECOWAS da AU sun gaza wajen yin Allah wadai da zababbun shugabannin da suka sauya doka domin tsawaita mulkinsu.
“Lokacin da wasunsu suka canza ka’ida don sake tsayawa takara karo na uku, ba mu ji ECOWAS ta yi Allah-wadai da hakan ba, me ya sa ECOWAS ba ta yi Allah-wadai da hakan ba? Me ya sa kungiyar Tarayyar Afirka ba ta yi Allah-wadai da hakan ba?”in ji Manuh.
Ba tare da la’akari da musabbabin juyin mulkin ba, masana sun ce juyin mulkin zai tsoratar da masu zuba jari daga yammacin Afirka.
A halin da ake ciki kuma, shugabannin kasashen yammacin Afirka sun yanke shawarar yadda za su dakile karin juyin mulki da kuma sa sojoji su koma bariki yayin da kasashen ke fama da matsalar rashin tsaro.