Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar NDLEA Ta Kwace Kwayoyi 22,160kg A Legas


An kama sama da kilogiram 22,160 na maganin kodin da kwayoyin methamphetamine da kuma tabar wiwi a tashar ruwa ta Apapa da kuma wani katafaren gidan kwayoyi mai suna Akala da ke Mushin a Legas.

Lamarin ya faru ne yayin wasu farmaki biyu da jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA suka gudanar a jihar.

Kakakin hukumar, Femi Babafemi, ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a jiya cewa 14,080kg na maganin kodin da kuma 4,352.43kg na hulunar kwayoyi da aka yi amfani da su wajen boye magungunan cikin wata kwantena mai kafa 40 da aka shigo da su daga Indiya. An kama su ne a ranar 2 ga Fabrairu a tashar jirgin ruwa ta Apapa.

Har ila yau, an kama tabar wiwi da aka shigo da su daga Ghana da kilogiram 3,727.72 na methamphetamine a wani samame da aka kai da sanyin safiyar ranar 3 ga watan Fabrairu a Akala, inda aka kama mutane 17 da suka hada da mata biyar a ranar 3 ga watan Fabrairu.

Babafemi ya ce an kama su ne a tashar jiragen ruwa na Legas biyo bayan bayanan sirri daga abokan huldar kasashen waje da hadin gwiwar masu ruwa da tsaki a tashar.

Jami’an hukumar NDLEA tare da goyon bayan sojoji sun kai farmaki kan wasu katafaren rumbunan ajiyar magunguna tare da kwashe jakkuna da kwalabe na wiwi, da na kwayar loud, da na methamphetamine da dai sauran miyagun kwayoyi da kuma kama mutane 17 da ake zargi don bincike,” a cewar sanarwar NDLEA din.

Sanarwar ta kara da cewa, an kama wata mace da ake zargi a matsayin shugaban masu safarar miyagun kwayoyi, Mrs Jemilat Seriki, wadda aka ce tana daya daga cikin masu mallakar kwalayen Loud 12,385 da aka shigo da su daga Ghana kuma aka kama su a Eko Atlantic Beach da ke Victoria Island a Legas a ranar 27 ga Nuwamba, 2021 bayan jami'an masu safarar miyagun kwayoyi suka shafe makonni suna farautarsu.

XS
SM
MD
LG