Wasu masu fama da larurar makanta 'yan asalin jihar Neja da gwamnati ta tura cibiyar koyar da masu fama da nakasa da ke Legas sun ce sun shiga wani hali na tsaka mai wuya a sakamakon rashin samun kudadensu na alawus-alawus da ya kamata a ce gwamnatin Nejan ta tura masu.
Yanzu sama da watanni tara ba a tura masu ko sisin kwabo ba.
Malama Mariya John na daya daga cikin makafi guda da ta ce ita 'yar asalin garin auna ta karamar hukumar Magama, ta kuma ce a yanzu suna samun abinci ne daga 'yan uwansu da suka je cibiyar ta Legas daga wasu jihojin Najeriya al’amarin da ta ce ya jefa su cikin wani hali.
A lokacin da mu ka tuntubi sakataren gwamnatin Jihar Nejan Alh. Ahmed Ibrahim Matane akan wadan nan makafi ya ce gaskiyar lamari ba su da labari akan lamarin makafin, amma zai gudanar da bincike akai.
Bayanai dai sun nuna cewa dukkanin masu fama da nakasa da suka samu zuwa wannan cibiya ta ba su horon akan sana’o’i daban daban dake lagas.
Sukan koma jihohinsu domin horarda wadanda basu samu zuwa ba, al’amarin dake taimaka masu wajan tafiyar da rayuwarsu ta yau da kullun.