Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Na Neman Toshe Kafafen Da Ake Sace Ma Ta Man Fetur Na Dala Biliyan 4 Duk Shekara


NUPRC
NUPRC

Sakamakon hauhawar farashin man fetur, Najeriya na daukar matakan dakile satar mai, a wani bangare na kokarin da kasar ke yi na maido da kudaden da ta yi asarar su.

Najeriya na asarar kusan ganga 150,000 na mai a rana sakamakon fasa bututun mai ana kwasa ba bisa ka'ida ba. A haka ne hukumomi suka ce kasar na asarar kusan dala biliyan hudu a duk shekara, wato kashi 10 na kasafin kudinta na shekara.

Shugaban Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya, Gbenga Komolafe ya sanar da wani yunkuri na kwato kudaden a wannan makon, amma ya ki bayar da karin bayani kan sabbin matakan da hukumomi za su dauka.

Gbenga ya ce Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya amince da shirin Samo Kudaden Shiga Na Daukacin Bangaren Man Fetur (Industry-Wide Oil Revenue Revenue Initiative, a Turance) tare da kafa kwamitin da ya hada da hukumomin tsaro da dama. Ya ce kwamitin zai fara aiki nan ba da dadewa ba.

"Za a shaida kyakkyawar tasirin hakan nan ba da jimawa ba saboda akwai tsarin hadin gwiwa don dakatar da lamarin, musamman ma yadda ya shafi kudaden tarayya. Kada ku yi tsammanin zan bayyana dabarun gwamnati," in ji Gbenga.

Hukumar da ke kula da albarkatun man fetur ta ce babban shirin farfado da tattalin arzikin kasar zai ninka yawan man da kasar ke hakowa daga ganga miliyan 1.5 a rana zuwa ganga miliyan 3 a ko wani lokaci.

Man da ake samu ya ragu sosai a Najeriya a shekarun baya bayan nan sakamakon fasa bututun mai ana kwasa ba bisa ka'ida ba. Hukumar ta ce yawan man da ake hakowa ya ragu zuwa ganga miliyan 1.5 a rana tun daga watan Disamban 2021 daga miliyan 1.7 a farkon shekarar da ta gabata.

Masanin harkokin makamashi Odion Omonfoman ya ce shirin dawo da kudaden na gwamnati abu ne mai yiyuwa.

Amma ya kuma kara da cewa duk da daukar wadannan matakan, dole ne hukumomi su yi la'akari da al'ummomin yankunan da ke fama da matsalolin muhalli sakamakon hako man fetur.

Farashin man fetur ya tashi a kasuwannin duniya zuwa sama da dala 90 kan kowace ganga. Tattalin arzikin Najeriya ya dogara ne sosai kan samun kudin shiga daga man fetur.

XS
SM
MD
LG