Hajiya Fatima Suleiman dake zama shugaban kungiyar Bayar Da Shawara Bisa Tsarin Musulunci ta Najeriya (Islamic Counselling Initiative of Nigeria, a Turance), ta ce shekaru goma kenan da ake gudanar da irin wannan taro don wayar wa al’umma kai kan kalubalen da mata dake sanya hijabi ke fuskanta da kuma hanyoyin magance su.
Wasu ‘yan mata dalibai da muryar Amurka ta zanta da su, sun ce hijabi na mutunta mata da ‘yan mata.
Ita ma Jesinta Nwobodo daga kungiyar CAN reshen matasa, da ta halarci taron, ta kara jaddada cewa kamar yadda addinin musuluncin ya tsara, shi ma addinin Kirista ya umurci mata su rufe jikinsu.