Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Yunkurin Juyin Mulki A Guinea Bissau


Shugaban Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embalo
Shugaban Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embalo

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, da yammacin ranar Talata, ya zanta da Umaro Sissoco Embalo, jim kadan bayan shugaban na kasar Guinea Bissau ya tsallake rijiya da baya a yunkurin da sojoji suka yi na hambarar da gwamnatinsa.

Shugaba Buhari ya taya Embalo murnar tsira daga yunkurin juyin mulkin, ya kuma yaba wa sojojin da ke biyayya ga kasar Guinea Bissau bisa nuna kishin kasa da suka yi, wanda ya kai ga nasarar da suka samu kan sojojin da ba su da rikon amana kamar yadda kakakinsa Malam Garba Shehu ya fada cikin wata sanarwa da Muryar Amurka ta samu kwafi.

Shugaban ya yi Allah wadai da yunkurin ruguza tsarin mulkin da aka kafa a kasar Guinea Bissau tare da mika fatan alheri da goyon bayan gwamnati da al'ummar Najeriya ga gwamnatin Guinea-Bissau da ma Shugaba Embalo.

"Ina fatan yin aiki tare da ku don karfafa alakar da ke tsakanin kasashen 'yan uwanmu, da kuma karewa da inganta dimokuradiyya da kimarta a fadin yankin, da ma nahiyar baki daya," a cewar Buhari ga Embalo.

A yayin tattaunawar, shugaba Embalo ya tabbatar wa shugaba Buhari cewa an shawo kan lamarin “komai lafiya lau yanzu, kuma an daidaita al’amura yadda ya kamata.

XS
SM
MD
LG