Hukumar tara kudaden shiga ta Najeriya ta fada a ranar Litinin din da ta gabata cewa ta hada gwiwa da kungiyar ‘yan kasuwa domin karbar harajin kayayyaki na (VAT) daga miliyoyin kananan ‘yan kasuwar, wani bangare na yunkurin fadada kudaden shiga da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ke yi.
Wasu mutane mazauna birnin Jos sun bada ra’ayoyinsu game da matsalar miyagun kwayoyi, a inda suke da kuma irin taimakon da yakamata a baiwa masu ta’ammali da kwayoyi.
A Najeriya magidanta kusan da dari biyu ne yanzu haka ke neman matsunni a sanadiyar ruwan sama da ya ruguza gidajensu a jihar kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya.
A birnin São Paulo na Brazil, wata sabuwar kwayar da ake yi da sinadari ta na daure kan hukumomi. Ana kiran kwarar da suna K9, kuma ta na da rahusa sosai, sannan ta na zamewa masu shanta jaraba.
Kasar Kamaru na yaki da safarar koko da auduga da kuma sauran kayan amfanin gona zuwa Najeriya, inda ta haramta cinikaya na wucin gadi bisa ka’ida na tsawon dan wani lokaci.
An zabi Burna a rukunin BET tare da Aya Nakamura, Ayra Starr, Central Cee, Ella Mai, KO, L7nnon, Stormzy, Tiakola da kuma Uncle Waffles.
A shekarun baya dai kasuwar ta Agiye ta yi fice wajen gudanar da kasuwanci dabbobi musammma ma a dai-dai irin wannan lokacin na Sallar Layya.
Bisa kididdigar da hukumar lafiya ta duniya WHO ta fitar, kusan dukkan mutane a duniya suna shakar iskar da ta zarce ka'idojin ingancin iska na hukumar lafiya ta duniya – wato isa da take a gurbace. Wannan gurbacewar yanayi na da illa ga lafiyar dan adam.
Mutane 16 ne aka kashe a wasu hare-hare biyu da aka kai a arewa maso tsakiyar Najeriya a yankin da ke fama da rikicin kabilanci, in ji rundunar sojoji.
A wata ziyara da suka kai ranar Litinin 19 ga watan Yuni 2023, hamshakin attajirin duniya Bill Gates da hamshakin dan kasuwa Aliko Dangote sun kai wa shugaba Tinubu ziyara a fadar shugaban kasa.
Shahararrun attajiran duniya, Bill Gate da Aliko Dangote sun kai ziyar Nijar inda suka gana da shugaban Kasar Nijar Mohamed Bazoum. Ganawar da ta mayar hankali kan batun karfafa huldar dake tsakanin Gidauniyoyinsu da Jamhuriyyar Nijar musamman kan batun kiyon lafiya.
Wani rahoton baya bayan nan ya nuna cewa kwararrun ma'aikatan lafiya a Ghana na yin kaura zuwa wasu kasashen waje, musamman Burtaniya, domin neman rayuwa mai inganci, abin da ke sanya tsarin kula da lafiyar jama'a ta kasar cikin mawuyacin hali.
A wani al'amari na baya-bayan nan, fitattun attajirai biyu na Najeriya, Aliko Dangote da Abdulsamad Rabiu, sun yi asarar dala biliyan 5.85 baki daya, kamar yadda cibiyar Bloomberg Billionaire Index (BBI) ta bayyana.
Majalisar Dattawa ta tabbatar da Nusrat Chowdhury, wata lauya mai kare hakkin jama'a, a matsayin Musulma ta farko da ta zama alkalin tarayya a tarihin Amurka.
Ana samun ciwon ne sakamakon doguwar nakuda yayin da da yake yunkurin fitowa, inda kuma mahaifiyar ba ta samun kulawar gaggawa da ta dace a asibiti.
Galibin mutane 108 da suka nutse bayan wani jirgin ruwa ya nutse a arewa ta tsakiyar Najeriya, mata ne da ‘ya’yansu, kamar yadda wadanda suka tsira da kuma hukumomin yankin suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press a ranar Alhamis yayin da aka kawo karshen aikin binciken ceton.
Tsohon gwabnan jihar Zamfara Sanata Abdulazeez Yari Yace taron dangi da aka masa yasa ya fadi zaben shugabancin majalisar dattawan Najeriya. Yari ya fadi hakanne a wata hira da muryar Amurka kan abinda yake ganin yasa baiyi nasara ba.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana nadin mukamai na musamman guda takwas, kamar yadda wata sanarwa da Daraktan yada labarai na fadar gwamnatin Najeriya Abiodun Oladunjoye ta bayyana.
Domin Kari