Kwale-kwalen na katakon yana dauke ne da mutane sama da 250 a kogin Neja a jihar Kwara yayin da suke dawowa gida daga wani daurin aure da daddare a lokacin da jirgin ya ci karo da gungume inda ya rabe biyu da sanyin safiyar Litinin din nan, in ji wadanda suka tsira.
Daya daga cikin wadanda suka tsira da rayukansu, Ibrahim Mohammed, ya ce sun ceto wasu kananan yara zuwa gabar teku, “amma wasu daga cikin matan wadanda ba su so barin ‘ya’yansu ba, sun nutse tare.
"Mafi yawan matan da ke cikin wannan kwale-kwalen suna da yara, (kuma a) yawancin mutanen da suka mutu mata ne da kananan yara," in ji Mohammed. Ya ce ya kubutar da yara uku amma ya rasa ‘yan uwansa tara.
Ya kara da cewa mutanen kauyen sun kawo karshen aikin ceton ne a ranar Alhamis da yamma, tare da binne wadanda abin ya shafa a kusa da kogin kamar yadda al’adar yankin ya tanada.
Akalla mutane 144 ne suka tsira da rayukansu a hatsarin a kogin Neja, wanda shi ne daya daga cikin mafi tsawo a Afirka mai nisan kilomita 4,100 (mil 2,500). Jirgin mai daukar mutane kusan 200 ne amma kuma ya dauki akalla mutane 250, inji Mohammed Ibrahim Liman, shugaban gundumar Pategi, inda hatsarin ya auku.
"Mutane sun yi naziri da gaggawa don ba da taimako, amma da wuya a gano fasinjojin idan aka yi la'akari da girman kogin," abin da Liman ya shaida wa AP kenan. Ya ce kusan 68 daga cikin wadanda suka mutu sun fito ne daga wani kauye.
Ana amfani da kwale-kwale don sufuri a Pategi da sauran al'ummomin da ruwa ya kewaye a fadin Najeriya. Hatsarin da ke tattare da su ya zama ruwan dare kuma galibi ana zarginsu da yin lodi fiye da misali da kuma amfani da jiragen ruwa da ba su da kyau. Wani jirgin ruwa da ya kife a watan Mayu ya kashe mutane 15 ciki har da yara.
Hatsarin na ranar Litinin na daya daga cikin mafi muni a Najeriya a cikin 'yan shekarun nan, in ji hukumomi.
Yayin da mazauna kauyen ke zaman makoki, sun yi kira ga hukumomi da su inganta hanyoyin da ke yankin a matsayin hanyar sufuri da aka fi so.
“Rayukan da aka rasa sun riga sun tafi. Ya kamata gwamnati ta yi duk abin da za ta iya don taimaka mana.” Inji Muhammed Alhassan, wanda ya rasa ‘yan uwa shida a hadarin.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta duba kalubalen da ke tattare da safarar ruwa a cikin kasa domin tabbatar da bin ka'idojin kiyaye lafiya.
Bayan da ya ziyarci gundumar Pategi a ranar Laraba, gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya ce jihar za ta fitar da karin ka'idojin kiyaye lafiya na sufurin ruwa.
“Matakinmu na gaggawa shi ne samar da akalla rigunan ceto guda 1,000 don tallafa wa tafiye-tafiye cikin lafiya a kan ruwa,” in ji gwamnan, a cewar wata sanarwa da ofishinsa ya fitar.
-AP