Rikici ya barke tsakanin makiyaya da manoma a jihar Filato, wanda ke kan iyaka tsakanin arewacin kasar inda galibi Musulmai ne da kuma kudancin Najeriya wadanda galibinsu mabiya addinin Kirista ne.
A wani sabon tashin hankalin da ya barke a ranar Talatar da ta gabata, wasu ‘yan bindiga sun kashe ‘yan kungiyar manoman yankin a gundumar Riyom, yayin da wasu mutane 10 suka mutu a wani hari da aka kai a yankin Mangu, in ji kakakin rundunar.
"An rasa rayuka shida a Riyom," Manjo Ishaku Takwa ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP a ranar Laraba.
"An kuma sake kai wani hari a wasu al'ummomi a Mangu inda mutane 10 suka mutu."
Dan Majalisar Jihar Filato mai wakiltar Mangu ta Kudu, Bala Fwangje, ya ce an kashe mutane 14 a yankin.
“Mun ji an kashe mutane kusan 14, an lalata gidaje, an kuma kona dukiyoyi amma har yanzu ban samu cikakken bayani ba,” inji shi.
Tun a watan Mayu, kusan mutane 200 ne aka kashe a rikicin da ya barke tsakanin al’ummar kabilar Berom, wadanda galibi Kiristoci ne, da kuma al’ummar Musulmi Fulani masu kiwo a yankunan Riyom, Barikin Ladi da Mangu na Filato.
Ba a dai san ko me ya jawo hare-haren na baya-bayan nan a Filato ba, amma kashe-kashen ramuwar gaya da ake yi tsakanin makiyaya da manoma yakan bazu har zuwa kauyukan da wasu gungun ‘yan bindiga dauke da muggan makamai ke yi wa jama’ar gari fashi da garkuwa da mutane da kuma kashe su.
Rikicin Filato na daya daga cikin kalubalen tsaro da shugaba Bola Tinubu ke fuskanta, wanda ya karbi ragamar mulkin kasar mafi yawan al'umma a Afirka a karshen watan Mayu.