Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Burna Boy Ya Zama Na Farko A Nahiyar Afrika Da Ya Ci Lambar Yabo Ta Fitattun Mawaka Bakaken Fata "BET AWARDS" Sau Hudu


Burna Boy ya lashe lambar yabo Ta Fitattun Mawaka Bakaken Fata "BET AWARDS
Burna Boy ya lashe lambar yabo Ta Fitattun Mawaka Bakaken Fata "BET AWARDS

An zabi Burna a rukunin BET tare da Aya Nakamura, Ayra Starr, Central Cee, Ella Mai, KO, L7nnon, Stormzy, Tiakola da kuma Uncle Waffles.

Shahararren Mawakin Najeriya, Burna Boy ya ci lambar yabo ta fitattun mawaka bakaken fata ta "BET AWARDS ta shekarar 2023.

Burna Boy ya ci lambar yabo Ta Fitattun Mawaka Bakaken Fata "BET AWARDS
Burna Boy ya ci lambar yabo Ta Fitattun Mawaka Bakaken Fata "BET AWARDS

Tauraron Burna Boy, wanda ya ke daya daga cikin fitattun mawaka da 'yan raye raye da kuma maruba wakoki a nahiyar Afrika, ya fara haskawa ne a shekara ta 2012, lokacin da ya fitar da wata waka da ake kira "Like to Party" daya daga cikin jerin wakokin da ke cikin wakokinsa na farko da ya fitar a dunkule. Koda yake bai halarci bikin ba, Burna ya riga ya sami lambobin yabo na fitattun mawaka bakaken fata "BET AWARDS" har sau uku shekarun baya, wato 2019, 2020 da 2021.

Burna Boy a bikin Coachella 2019
Burna Boy a bikin Coachella 2019

Haka kuma ya sami lambar yabo ta makawakan Afrika da suka fi fice a bukin yaba fitattun makwa na VGMA a shekara ta 2020.

An haifi Burno Boy, dan shekaru 29, ranar 2 Juli, 1991 a garin Patakwal na jihar Ribas. Ya kuma a tsakanin mawakan Najeriya da kuma sauran kasashen nahiyar Afrika ya shahara wajen yawan fadan ra'ayinsa kan batutuwa masu sarkakiya.

XS
SM
MD
LG