Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Marasa Lafiya A Ghana Na Cikin Hatsari Saboda Kaurar Da Wasu Ma'aikatan Lafiya Ke Yi Zuwa Birtaniya


Wasu ma'ikatar jinya
Wasu ma'ikatar jinya

Wani rahoton baya bayan nan ya nuna cewa kwararrun ma'aikatan lafiya a Ghana na yin kaura zuwa wasu kasashen waje, musamman Burtaniya,  domin neman rayuwa mai inganci, abin da ke sanya tsarin kula da lafiyar jama'a ta kasar cikin mawuyacin hali.

Patience Arthur da tayi aikin nas kusan shekara goma sha hudu a Ghana, na daya daga cikin nas nas a Ghana da suke shirin yin kaura zuwa kasar waje domin aikin nas sakamakon matsalar da ta ce suna fama da ita ta rashin inganta yanayin aikinsu, ciki har da karancin albashi da rashin isasshen kayan aiki.

"albashinmu ya yi karanci kuma mun samu labarin cewa kawayenmu suna samun albashi mai tsoka a kasashen waje, kuma suna aiki a wurare masu kayatarwa" inji ta.

Tuni kaurar ma'aikatan jinya ta fara tasiri akan harkar lafiya ta kasar.

Wasu ma'ikatar jinya
Wasu ma'ikatar jinya

Daga babban asibitin komfo Anokye dake birnin Kumasi a yankin Ashanti, daya daga cikin kwararrun nas nas a asibitin da ta bukaci da a sakaya sunanta ta fada wa Muryar Amurka cewa kaurar da kawayensu ke yi na mummunan tasiri wajen aikinsu "muna gajiya yanzu sabida muna zuwa mutum uku ko hudu amma kaurar da wasu kawayenmu su ka yi ta sa yanzu haka aiki na yi mana yawa"

Dakta Imoro Faisal mai sharhi kan harkar kiwon lafiya kana likita a asibitin South Suntreso da ke yankin Ashanti na kudancin Ghana ya bayyana cewa;

"idan ya kasance ma'aikatan lafiya suna zuwa kasashen waje, hakan zai kawo karancin ma'aikata kuma zai sanya aikinmu cikin halin koma baya. Za ka iya zuwa wani asibiti ka tarar da an samu raguwar ma'aikatan jinya. Hakan ya janyo matsala sosai. Matakin da ya kamata gwamnati ta dauka shi ne ta inganta yanayin aikin ma'aikatan jinya. Ya kasance ta samar musu abinda suke bukata domin ganin basu isa kasashen waje ba|, inji shi.

Shi kuwa Issah Abubakar babban jami'i a hukumar samar wa al'ummar kasar Inshorar lafiya a yankin Ashanti ya ce gwamnati na nata iya bakin kokari domin inganta yanayin aikin ma'aikatan lafiya ta kasa

"gwamnati ta dauki matakai da dama ciki har da tinkarar asusun IMF domin neman tallafi kuma babban bankin duniya da kasar Amurka duk suna shirin taimaka ma Ghana wajen ganin ta farfado daga matsalar tattalin arziki da ta tsunduma a ciki. Muna bai wa ma'aikatan jinya na kasa hakuri kuma nan bada jimawa ba komai zai daidaita"

Ƙwararrun ma'aikatan jinya da yawa sun sulale sun bar ƙasar da ke yankin Afrika ta Yamma don samun ingantattun ayyuka mafi tsoka a ƙasashen waje.

A cikin 2022, ma'aikatan jinya 'yan Ghana fiye da 1,200 ne suka shiga Birtaniya.

Saurari rahoton Hamza Adams:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:15 0:00
XS
SM
MD
LG