Alhazai fiye da dubu hudu{4,000} ne aka kwantar a asibiti sakamakon tsananin zafin rana a yayin aikin hajjin bana, cewar mai wani Magana da yawun ma'aikatar lafiya ta kasar a jiya laraba.
Dr. Muhammed Al-Abd Al-Aali ya kuma kara da cewa, yawan alhazan da suka fuskanci matsalar tsananin zafin ranar ya wuce dubu shida da dari bakwai {6,700}
‘Mun shaidawa alhazai cewa kar su dauki kaya zuwa wurin jifa, da zuwa masallacin Ka’aba, sannan su kula da tafiya cikin natsuwa da kauce ma shiga turmutsitsi.
A ranar Arfa alhazai sun rika amfani da laima, yayin da zafin rana ya kai maki 45 a ma’aunin yanayi
Hukumomin Saudiyya dai sun samar da dubban ma’aikatan lafiya domin kula da alhazai a bana, yayin da masu aikin sa kai ke raba ruwan sha.
~ Hauwa Sheriff