Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nusrat Chowdhury Ta Zama Musulma Ta Farko Da Ta Zama Alkalin Tarayya A Tarihin Amurka


Nusrat Chowdhury
Nusrat Chowdhury

Majalisar Dattawa ta tabbatar da Nusrat Chowdhury, wata lauya mai kare hakkin jama'a, a matsayin Musulma ta farko da ta zama alkalin tarayya a tarihin Amurka.

Za ta kasance a wannan matsayi na tsawon rayuwarta a kotun tarayya ta Brooklyn da ke New York bayan kada kuri'a 50-49 ranar Alhamis bisa ga jam’iyya.

Tabbatar da mukamin na ta ya janyo yabo daga Ƙungiyar 'Yancin Jama'a ta Amurka, inda ita ce darektan shari'a na ACLU na Illinois. Kafin wannan matsayi, ta yi aiki daga 2008 zuwa 2020 a ofishin ACLU na kasa, ciki har da shekaru bakwai a matsayin mataimakiyar darektan Shirin Tabbatar Da Adalcin launin fata na ACLU.

ACLU
ACLU

A cikin wani sakon tuwita, ACLU ta kira ta "lauyar kare hakkin jama'a da ta yi fice.”

Shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa Chuck Schumer, D-N.Y, wanda ya nemi a zabe ta, ya ce ta kafa tarihi a matsayin Ba’amurka ‘yar asalin Bangladesh ta farko kuma Musulma Ba’amurka ta farko da ta zama alkali ta tarayya.

Bayan kammala makarantar shari'a, Chowdhury ta yi aiki a birnin New York a matsayin alkalin gundumar Amurka.

Ta kuma yi aiki a Kwamitin Aiki Da Cikawa Na Shugaban Kasa kan Tabbatar Da Amincewar Jama'a a Tsarin Adalci na Amurka.

Nadin nata ya yi daidai da alkawarin da Shugaba Joe Biden ya yi na jaddada tsarin tafiya da kowani jinsi ko launi a nade-naden fannin shari'a.

~AP

XS
SM
MD
LG