Wannan na zuwa ne lokacin da dubban ‘yan gudun hijira ke fama da halin da suka tsinci kansu na rashin muhallansu a jihar da wasu sassan arewacin Najeriya.
Samun ingantaccen mazauni abu ne da kan iya saukakawa tare da kyautata rayukan mazauna wuraren, kuma akasin haka kan iya jefa rayukan su cikin mummunan yanayi.
Yanzu haka magidanta kusan da dari biyu ne suka samu kansu cikin halin rashin mazauni mai inganci sanadiyar ruwan sama tare da iska mai tsanani a garin Zauro na jihar kebbi dake arewa maso yammacin Najeriya.
Malam Arabiyu, daya daga cikin magidanta da suka hadu da wannan ibtila'in ya shafa ya ce hasarar da suka yi tana da yawa.
Musa Bello Dikkon Zauro ya ce lamarin ya haifar da rudani da fargaba ga jama'ar garin.
Zayyanu Gado jami'in da ya wakilci karamar hukumar Birnin Kebbi da ya ziyarci garin na Zauro ya ce sun kiyasta gidaje kusan dari biyu da abin ya shafa.
Masana muhalli sun ce akwai wasu abubuwa da jama'a ke aikatawa wadanda akasari sune ke haifar irin wannan matsala da ta faru tun a farkon damina.
Dokta Yusuf Isah Masani ne akan kare muhalli ya ce matsalar sauyin yanayi ta na gaba-gaba cikin matsalolin da duniya ke fuskanta, kuma wasu abubuwa da jama'a ke aikatawa na taimakawa ga wanzuwar matsalar .
Wannan matsalar ta faru ne lokacin da dubban ‘yan gudun hijira ke fama da yanayin da suka samu kansu na rashin muhallansu na asali.
Ko a makon da ya gabata mataimakin gwamnan na kebbi Sanata Umar Abubakar Tafida, sai da ziyarci kananan hukumomin Fakai da Sakaba inda ya jajantawa ‘yan gudun hijira fiye da dubu uku tare da basu tallafi domin saukaka halin da suka samu Kan su a ciki.
‘Yan gudun hijira da yawa ne ke fuskantar matsalolin rayuwa saboda raba su muhallansu na asali, abin da ke nuna damuwa da wadanda suka rasa muhallansu ke shiga a sassa daban daban na Najeriya.
Saurari shirin a sauti: