Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bill Gates Da Aliko Dangote Sun Ziyarci Tinubu A Fadar Shugaban Kasa Da Ke Abuja


Bill Gates Da Aliko Dangote Sun Ziyarci Tinubu
Bill Gates Da Aliko Dangote Sun Ziyarci Tinubu

A wata ziyara da suka kai ranar Litinin 19 ga watan Yuni 2023, hamshakin attajirin duniya Bill Gates da hamshakin dan kasuwa Aliko Dangote sun kai wa shugaba Tinubu ziyara a fadar shugaban kasa.

Makasudin ziyarar tasu dai shi ne mika sakon taya murna ga shugaba Tinubu kan nasarar da ya samu na zama shugaban Najeriya na 16 da kuma tattaunawa kan kokarin da gidauniyarsu ke yi a Najeriya.

Gidauniyar biyun na Gate da Dangote sun himmatu wajen inganta fannin kiwon lafiya a kasar tare da yin alkawarin ci gaba da ba da goyon baya don kara kyautata fannin ga ‘yan Najeriya.

Bill Gates Da Aliko Dangote Sun Ziyarci Tinubu
Bill Gates Da Aliko Dangote Sun Ziyarci Tinubu

A yayin ziyarar, Aliko Dangote ya yi jawabi ga manema labarai da suka halarci taron inda ya bayyana muhimman batutuwan da suka tattauna.

Ya bayyana cewa makasudin ziyarar tasu ita ce taya shugaba Tinubu murnar nasarar zabensa da kuma yi masa bayani kan ayyukan gidauniyar Bill and Melinda Gates da gidauniyar Aliko Dangote a Najeriya.

Aliko Dangote
Aliko Dangote

Dangote ya jaddada kudirinsu na inganta fannin kiwon lafiya a Najeriya tare da bayyana himmar gidauniyar ta kara yin ayyuka a kasar. Ya kuma bayyana cewa suna sa ran samun hadin kai daga gwamnati tare da bayyana aniyarsu ta mara wa shugaba Tinubu baya domin cimma burinsa da manufofinsa.

Dangote ya yaba wa shugaban kasar kan ayyukan da ya yi, kamar sabon tsarin kasuwanci na Forex da kuma cire tallafin mai, inda ya bayyana cewa abubuwa ne masu kyau da za su ba da damar samun karin kudade ga ilimi, samar da kayayyakin kiwon lafiya, da sauran fannoni.

Bill Gates Da Aliko Dangote Sun Ziyarci Tinubu
Bill Gates Da Aliko Dangote Sun Ziyarci Tinubu

Ziyarar da Bill Gates da Aliko Dangote suka kai a fadar shugaban kasa ba wai kawai na nuna yadda shugabannin kasashen duniya ke son ci gaban Najeriya ba ne, har ma da nuna muhimmancin hadin gwiwa wajen samar da ci gaba mai dorewa.

A yayin da Najeriya ke sa ran samun makoma mai kyau, hadin gwiwa tsakanin gwamnati, manyan gidauniyoyi, da fitattun mutane irinsu Gates da Dangote ya share fagen samar da ci gaba mai inganci, tare da inganta harkokin kiwon lafiya, ingantaccen ilimi, da ingantattun ababen more rayuwa domin ci gaban al'ummar Najeriya.

~ Yusuf Aminu

XS
SM
MD
LG