Wasu mutane goma sha biyu da suka tsallake rijiya da baya a yunkurin yin kaura ta hanyar teku zuwa Turai sun samu saduwa da iyalansu a Senegal, mako guda bayan an gano su a tekun Atlantika na kasar Cape Verde.
Kasar Habasha za ta hada kai da mahukuntan Saudiyya domin gudanar da bincike kan zargin da wata kungiyar kare hakkin bil'adama ta yi cewa, jami'an tsaron kan iyakar kasar sun kashe daruruwan bakin haure daga kasar, kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen kasar ta sanar a ranar Talata.
Yayin da ECOWAS ta yanke shawara kan ranar da za ta aika dakarunta zuwa Nijar, bayan taron kwana biyu a birnin Accra, shugaban jam'iyyar adawa ta GUM, Rev. Christian Kwabena Andrews ya yi barazanar yin da zanga-zanga idan har Gwamnatin Ghana ta baiwa ECOWAS dakaru soja domin yaki a Nijar.
Shugabannin Musulmai, a karkashin jagorancin limamin limaman Ghana, Dakta Sheikh Usman Nuhu Sharubutu, sun yi kira da kada a dauki matakin soja wajen maido da mulkin dimokradiya a kasar Nijar, domin zai kawo asarar rayuka.
A ranar 26 ga watan Yuli ne wata gwamnatin soji da ke kiran kanta Majalisar Tsaro ta Kasa, ta kaddamar da wani juyin mulki a Nijar tare da kama shugaba Mohamed Bazoum. Tun daga wannan lokaci ake tsare da Bazoum da iyalansa ba bisa ka'ida ba a fadar shugaban kasar da ke Yamai.
‘Yan Najeriya da dama dai sun fara dasa alamar tambaya a kan ko Shugaba Tinubu zai rika martaba tsarin mulkin dimokradiyya.
A Nijar, inda aka samu juyin mulki sannan aka kakaba wa kasar jerin takunkumai, ayyukan kungiyoyin jinkai ya ragu sossai, lamarin da ya jefa al’ummomin da suke ba su tallafi cikin takaici.
Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Linda Thomas-Greenfield ta ce: "An shafe kwanaki 100 kenan tunda fada tsakanin Sojojin Sudan da Dakarun Ba da Agajin Gaggawa ya barke, kuma a wannan lokacin, tashe-tashen hankula na rashin fahimta sun haifar da wahalhalu da ba a taba tsammani ba."
Rundunar Sojin Najeriya ta yi wa dakarunta kashedi dangane da takon-saka da ke wanzuwa tsakanin gwamnatin Sojin Jamhuriyar Nijar da kungiyar ECOWAS.
Kungiyar Kare Hakkokin Tattalin Arziki SERAP ta maka shugabanin Majalisar Dokokin kasa Godswill Akpabio da Tajudeen Abbas a kotu kan abinda ta kira haramtaccen shirin kashe Naira biliyan 40 domin sayen motocin silke 465 da kuma Naira biliyan 70 a matsayin tallafi wa yan majalisar.
Wani kwale-kwale ya nutse a tekun Sfax mai tashar jiragen ruwa na kasar Tunisiya, inda mutane biyar suka mutu, wasu bakwai kuma suka bace, in ji jami'ai a jiya Talata.
Masu rajin kare hakkin bil’adama a Nijar sun ce sun kasa samun damar ganawa da manyan jami’an siyasa da aka tsare bayan da sojojin juyin mulki suka hambarar da zababben shugaban kasar ta Afirka kusan makonni uku da suka gabata.
‘Yan kasuwar yankin arewacin Najeriya na ci gaba da bayyana zullumi saboda barazanar da dukiyar su ke fuskanta, yayin da iyakokin Najeriya da Nijar ke ci gaba da zama a garkame biyo bayan takunkumin cinikayya da kungiyar ECOWAS karkashin shugaba Tinubu ta sanya akan Jamhuriyar ta Nijar .
Wani jirgin saman rundunar sojojin saman Najeriya ya yi hadari inda ya rikito a wani kauyen jihar Neja a ranar jiya Litinin.
Da alamar wata kofa ta bude don tattaunawa tsakanin kungiyar ECOWAS da sojojin da su ka yi juyin mulki a janhuriyar Nijar da sauran masu ruwa da tsaki. Wannan ya biyo bayan ziyarar shiga tsakani da wasu manyan malaman Najeriya su ka kai.
Kungiyar Dillalan Man Fetur mai zaman kanta ta Najeriya ta ce farashin man fetur zai cigaba da karuwa muddin dalar Amurka ta tashi a kasuwar canji, amma kwararru a fannin tattalin arziki na cewa akwai mafita.
Babban hafsan Mayakan kasa Lt. Gen. Taoreed Lagbaja da babban hafsan hafsoshin kasar Lt. Gen. Christopher Musa ne suka tabbatar da hakan a Sakkwato lokacin da suka rako tsohon Babban hafsan mayakan kasa Lt. Gen. Faruk Yahaya jihar sa ta haihuwa bayan ajiye aiki.
Tawagar manyan malaman Islama na Najeriya da ta gana da shugaban gwamnatin sojan Nijar Janar Abdourahmane Tchiani ta ayyana nasarar ziyarar.
Domin Kari