Karar ta zo ne a daidai lokacin da Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya bayyana wa duniya cewa, akawun Majalisar Magaji Tambuwal ya aikawa wa 'yan Majalisar da alawus na hutu yayin da 'yan Najeriya ke fama da matsanancin talauci.
SERAP ta ce kididdiga ya nuna cewa mutane miliyan 137 ne ke fama da mumunan rashi da talauci, saboda haka ta ke so a dakatar da Majalisar daga kashe wadanan makudan kudade domin ya saba wa kundin tsarin mulkin kasa da kuma hakkokin bil'adama na duniya.
A hirar shi da Muryar Amurka, dan Majalisar wakilai Abubakar Hassan Fulata ya ce wadannan kudade da ake korafi akai ba kyauta ba ne. Bisa ga cewar shi, , mukamin sa a matsayin shi na dan Majalisar Wakilai ya fi na Minista, duk da haka bashi za a bashi motar. Fulata ya ce za a cire kudin motar a cikin albashin sa har zuwa lokacin da ya gama biya. Ya kumaabayyana cewa, gwamnati tana saya wa Ministoci motoci fiye da 10 amma ‘yan Najeriya ba su yi korafi akan wannan ba. Fulata ya ce duk abinda aka bashi a Majalisa an ba shi hakkin sa ne na dan Majalisa.
A nasa bayanin, gagarabadan Majalisar Dattawa, Ali Ndume, ya ce wannan abu da ake cece-kuce akai, abu ne da aka saba yi a Majalisa. Ya ce tunda aka fara dimokradiya a Najeriya ake saya wa 'yan Majalisa motoci domin yin aiki, kuma haka ake biyan su albashin su da hakokkin su, saboda haka ba sabon abu ba ne.
Da yake tsokaci kan batun, masanin harkokin Shari'a Mainasara Umar ya yi bayani cewa, sashi na 15 sakin sashi na 5 na Kundin tsarin mulkin kasa ya dora wajibci a kan duk wata hukuma ta yaki cin hanci da rashawa, saboda haka idan SERAP ta je kotu akan wannan magana ta yi daidai. Mainasara ya ce kotu ce za ta yi amfani da kashi 36 na kundin tsarin mulkin kasa, ko ta ce 'yan Majalisa sun yi daidai ko ba su yi daidai ba.
Kotun da aka shigar da karar dai ba ta sa ranar da za a saurari karar ba.
Saurari cikakken rahoton:
Dandalin Mu Tattauna