Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dole Mu Warware Rikicin Jamhuriyar Nijar Cikin Lumana


Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar
Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar

A ranar 26 ga watan Yuli ne wata gwamnatin soji da ke kiran kanta Majalisar Tsaro ta Kasa, ta kaddamar da wani juyin mulki a Nijar tare da kama shugaba Mohamed Bazoum. Tun daga wannan lokaci ake tsare da Bazoum da iyalansa ba bisa ka'ida ba a fadar shugaban kasar da ke Yamai. 

Kasar Nijar da ake ganin tana da kwanciyar hankali a tsakiyar yankin Sahel, ta sha fama da juye-juyen mulki tun a shekarar 1960, lokacin da ta samu 'yancin kai daga Faransa. Tabbas, mika mulki bayan nasarar da Mohamed Bazoum ya samu a zaben kansa shekaru biyu da suka gabata ya kasance cikin kwanciyar hankali, ba tare da nuna akwai wani rudani a kasa ba.

Juyin mulkin dai ya sa kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika, ko ECOWAS, ta yi kira da a maido da tsarin mulkin kasar ya zuwa da ranar 6 ga watan Agusta. A lokacin da wa'adin ya cika, kungiyar ECOWAS ta ba da umarnin a fara shiri tare da tura rundunar tsaron yankin domin maido da zaman lafiya a Nijar.

Mataimakin mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka Vedant Patel ya ce "ECOWAS ta nuna matukar jagoranci a tun farkon wannan rikicin, kuma Amurka ta yaba da aikinsu da shugabancinsu."

“ECOWAS ma ta fito fili cewa daukar matakin soja shi ne mataki na karshe bayan an gaza cimma fahimta, abin da muma muka yarda da shi. Kuma muna ci gaba da mai da hankali kan neman mafita ta hanyar diflomasiyya, muna kuma tuntubar ECOWAS da shugabanninsu kan wannan batu.”

Game da martanin tura dakarun ECOWAS, shugabannin juyin mulkin sun sanar da cewa, sun shirya gurfanar da shugaba Bazoum a gaban kuliya bisa laifin cin amanar kasa da kuma zagon kasa ga tsaron ciki da na wajen Nijar.

"Mun ji takaicin rahotannin cewa batun tsare Shugaba Bazoum ba bisa doka ba ya wuce yadda ake tunani, kuma yanzu (Majalisar Tsaro ta Kasa) tana barazanar gurfanar da shi gaban kuliya," a cewar kakakin Patel.

“Wannan matakin bai dace ba kuma babu hujja, kana a gaskiya, ba zai taimaka wajen warware wannan rikicin cikin lumana ba. Wannan karin cin fuska ne, a ra’ayinmu, ga dimokradiyya da adalci da mutunta doka. Kuma barazana irin wannan na nuna bukatar gaggauta mutunta tsarin mulki a Nijar.”

Kakakin Patel ya ce "Daga karshe, dukkanmu baki daya mun dace a kan warware wannan rikici cikin lumana da kuma kiyaye tsarin mulkin Nijar." "Muna sa ran ganin babu abin da zai taba Shugaba Bazoum da iyalansa, muna sa ran ganin an sako su, kuma muna sa ran ganin an mutunta tsarin mulkin Nijar da gaggawa."

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG