Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 5 Sun Mutu, 7 Sun Bace Bayan Nutsewar Kwale-Kwale Dauke Da Bakin Haure A Gabar Tekun Tunisiya


Kwale-kwale dauke da bakin haure
Kwale-kwale dauke da bakin haure

Wani kwale-kwale ya nutse a tekun Sfax mai tashar jiragen ruwa na kasar Tunisiya, inda mutane biyar suka mutu, wasu bakwai kuma suka bace, in ji jami'ai a jiya Talata.

Kakakin kotun Sfax Faouzi Masmoudi ya ce an ceto bakin haure 23 daga cikin mutane 35 da ke cikin jirgin, yawancinsu 'yan kasar Tunusiya da kuma "kadan 'yan kasashen hamadar Sahara."

Masmoudi ya ce kwale-kwalen ya nutse ne a ranar Litinin jim kadan bayan tashinsa daga yankin ta Sfax.

Kotun Sfax ta bude bincike don gano musabbabin hadarin, wanda ya faru kwanaki biyu bayan wani kwale-kwalen bakin haure ya nutse a gabar tekun Gabes da ke kudu maso gabashin Tunisiya mai tazarar kilomita 150 daga Sfax, lamarin da ya yi sanadin mutuwar wani yaro da kuma wani dan shekaru 20. Har yanzu ba a gano wasu mutane biyar ba.

A baya-bayan nan, kwale-kwale da dama sun kife a gabar tekun Arewacin Afirka da kuma kusa da gabar tekun Italiya. Dubun dubatar bakin haure sun sha yunkurin tsallaka tekun Mediterrenean a wannan shekara da nufin isa Turai.

Mahukuntan kasar sun ce bakin hauren da masu fasa kauri suka dauko cikin wasu kwale-kwale marasa karfi a gabar tekun Tunisiya sun sauka a wasu kananan tsibiran Italiya guda uku a cikin kwanaki biyu. A gefe guda kuma, wani jirgin ruwa na agaji ya gudanar da ayyukan ceto mutane sau 15, kuma jami'an tsaron gabar tekun Italiya a ranar Lahadin da ta gabata sun gano wata gawa a yammacin gabar tekun Sicily daga wani jirgin ruwa da ya nutse.

A makon da ya gabata, wani jirgin ruwan kasuwanci ya kwaso wasu mutane hudu da suka tsira da suka nutse a cikin wani kwale-kwale na masu fasa-kwauri. Sun ba da labarin yadda aka jefa su cikin tekun lokacin da igiyar teku ta mamaye jirginsu kuma fasinjoji 41 suka mutu.

~AP

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG