Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

JUYIN MULKIN NIJAR: Kungiyar Kare Hakkin Bil'adama Ta Ce Ta Kasa Ganawa Da Jami'an Da Ke Tsare


Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar
Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar

Masu rajin kare hakkin bil’adama a Nijar sun ce sun kasa samun damar ganawa da manyan jami’an siyasa da aka tsare bayan da sojojin juyin mulki suka hambarar da zababben shugaban kasar ta Afirka kusan makonni uku da suka gabata.

Jami'an sojin da suka yi wa Shugaba Mohamed Bazoum juyin mulki sun kuma kama wasu tsofaffin Ministocin gwamnati da wasu shugabannin siyasa kamar yadda Ali Idrissa, babban sakataren wata kungiyar kare hakkin bil'adama ta cikin gida ya bayyana. Bukatun ganinsu da duba lafiyarsu ya ci tura, in ji shi.

Tun a ranar 26 ga watan Yuli ne gwamnatin mulkin sojan da ta kwace mulki ta tsare Bazoum da matarsa da dansa a gidansu da ke babban birnin kasar. Ta ce tana shirin gurfanar da Bazoum a gaban kuliya bisa "cin amanar kasa" da kuma zagon kasa ga tsaron kasa, laifukan da suka cancanci hukuncin kisa a Nijar.

Mohamed Bazoum
Mohamed Bazoum

Kanar Maj. Amadou Abdramane, mai magana da yawun gwamnatin mulkin sojan ya bayyana a wani gidan talabijin da yammacin Lahadin da ta gabata yana mai cewa, ana kula da jami’an da ake tsare da su cikin mutuntaka kuma ba su nuna wata damuwa ta rashin lafiya ba. Wakilan jagororin juyin mulkin ba su yi gaggawar amsa tambayoyi kan ko za a bar kungiyoyin kare hakkin su kai ziyara ko tattaunawa da Bazoum da sauran su ba.

Colonel Major Amadou Abdramane
Colonel Major Amadou Abdramane

Juyin mulki dai ya yi kamari a yankin Sahel, kuma makwabciyarta Burkina Faso da Mali kowannensu sun sami juyin mulki har sau biyu tun daga shekarar 2020, amma ba su fuskanci tirjiya da matsin lamba daga kasashen duniya kamar na Nijar ba.

Kungiyar kasashen yammacin Afirka da aka fi sani da ECOWAS ta yi barazanar yin amfani da karfin soji idan ba a maido da Bazoum kan mukaminta ba, kuma ta kaddamar da rundunar tsaro na cika aiki domin dawo da zaman lafiya a Nijar. Majalisar mulkin sojan da ta ki amincewa da tawagar ECOWAS ta shiga cikin kasar, ta fada a yammacin Lahadin nan cewa a shirye take ta tattauna da kungiyar.

Taron ECOWAS.
Taron ECOWAS.

Sai dai a wata sanarwa ta gidan talabijin din kasar, mai magana da yawun Abdramane ya ce sabuwar gwamnatin da gwamnatin mulkin soji ta kafa ta sauke jakadan Nijar daga mukaminsa a makwabciyarta Ivory Coast, daya daga cikin mambobi 15 na kungiyar.

Matakin wani martani ne ga shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Ouattara wanda ya nuna "kosawarsa" na shiga tsakani na soji "da nufin kiyaye muradun da a yanzu ba su dace da na Nijar ta yau ba," in ji Abdramane.

Hafsan hafsoshin tsaron Yammacin Afirka na shirin ganawa a ranakun Alhamis da Juma'a domin tattauna wa kan juyin mulkin, kamar yadda kakakin kungiyar ECOWAS ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press. Wannan dai shi ne karo na farko da aka yi irin wannan taro tun bayan da kungiyar ta bayar da umarnin aikewa da dakarun da ke jiran cika aiki.

Da alama rundunar sojin jiran cika aiki zata sami dubban sojoji da dama daga kasashen da suka hada da Ivory Coast, Najeriya, Benin da Senegal. Babu tabbaccin, ko a yaushe ne, ko kuma idan za a aika da sojojin zuwa Nijar.

Kwamitin zaman lafiya da tsaro na kungiyar Tarayyar Afirka ya gana a jiya Litinin domin tattauna halin da ake ciki a Nijar amma ba ta bayyana wani mataki ba. Majalisar za ta iya yin galaba a kan kungiyar Tarayyar Afirka ta Yamma idan ta yi tunanin tsoma bakin soji na barazana ga zaman lafiya da tsaro a nahiyar.

Ana sa ran sabuwar jakadiyar Amurka a Nijar, Kathleen FitzGibbon, za ta isa birnin Yamai a karshen mako, a cewar wani jami'in Amurka. Amurka ba ta da jakada a kasar kusan shekaru biyu da su ka shude, abin da wasu masana Sahel suka ce ya bai wa Amurka karancin damar samun manyan 'yan siyasa da kuma bayanai.

~AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG