Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NEJA: Jirgin Saman Rundunar Sojojin Saman Najeriya Ya Yi Hadari a Shiroro


Jirgin mai saukar angulu
Jirgin mai saukar angulu

Wani jirgin saman rundunar sojojin saman Najeriya ya yi hadari inda ya rikito a wani kauyen jihar Neja a ranar jiya Litinin.

Jim kadan bayan tashinsa ne jirgin yayi hadari a yankin na Chukuba dake yankin karamar hukumar Shiroro a jihar Neja.

Jirgin mai saukar angulu samfurin MI-717 wanda ke ayyukan jigilar wadanda su ka jikata a fafatawar da dakarun kasar ke yi da yan bindiga a jihar Neja, ya fado ne da misalin karfe daya na ranar jiya Litinin a kusa da kauyen Chukuba.

Kakakin hedkwatar rundunar sojojin saman Najeriya AIR COMMANDER Edward Gakwet ya shaidawa muryar Amurka cewa, jirgin ya tashi ne daga makarantar firamare dake Zungeru a kan hanyarsa zuwa Kaduna inda ya yi hatsarin jim kadan bayan tashinsa a yankin Chukuba dake yankin karamar hukumar Shiroro a jihar ta Neja.

A dai dai lokacin da wakilinmu a Abuja ke aiko da wannan rahoto jami'ai na can su na kokarin ceto wadanda ke cikin jirgin.

Tuni dai mahukuntan rundunar sojojin saman Najeriyar su ka kaddamar da bincike don gano musabbabin aukuwar hatsarin.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG