Reverend Christian Kwabena Andrews wanda aka fi sani da Osofo Kyiri Abosom, ya yi wannan kalaman ne a taron manema labarai a Accra.
"Mun zo nan ne don bada shawara da kuma sa hannu kan wannan takardan dangane da shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo Addo da kada ya biye wa ECOWAS wajen tura Sojoji Ghana zuwa Niger. Baza mu goyi bayansa ba a matsayin mu 'yan kasar Ghana. Ina shaida wa Akuffo Addo da duk wani dan kasar Ghana cewa mu nisanci wannan shawara mara amfani da kungiyar ECOWAS ta dauka na tura sojojin mu zuwa Nijar. Kada wanda ya isa ya yi caca da rayukan sojojin mu. Kuma idan shugaban kasa ya ki saurarenmu sai wani abu ya faru, mu 'yan jami'iyyar GUM za mu fara zanga-zangar nuna kyama ga shugaban kasa da gwamnatinsa."
A gefe daya kuma Shugaban babban jam’iyyar adawa a Ghana (NDC), Johnson Asiedu Nketiah, ya gargadi shugaban kasar Nana Addo Dankwa Akufo-Addo game da tura sojojin Ghana zuwa Nijar, wadda take fama da juyin mulkin a halin da ake ciki yanzu.
Asiedu Nkatia ya ce zai gaya wa Shugaban Ghana Nana Akufo Addo da duk mutanin Ghana su kula, kada a dauki rayukar 'yan uwanmu sojoji a yi caca da su, a kan wannan matakin da bashi da amfani kwata-kwata.
Haka kuma mafi yawancin mutanen Ghana ba su da ra'ayin aika sojoji domin a yaki Nijar.
Mallam Adib Sani masanin tsaron da al'ammurra siyasar kasa da kasa ya ce duba da matsalolin tabarbarewar tattalin arziki da matsalolin tsaro da suka addabi kasashen yammacin Afrika, musamman Najeriya dake fama da Boko Haram da sauran kungiyoyin 'yan ta'adda da kuma matsalar rashin tsaron daga arewa maso gabashin Ghana, babu wani yaki da zai iya faruwa.
Saurari rahoton Hawawu Abdul Karim Young Pioneer:
Dandalin Mu Tattauna