Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Habasha Ta Ce Za Ta Binciki Zargin Kashe Bakin Haure Tare Da Hukumomin Saudiyya


Wasu bakin haure
Wasu bakin haure

Kasar Habasha za ta hada kai da mahukuntan Saudiyya domin gudanar da bincike kan zargin da wata kungiyar kare hakkin bil'adama ta yi cewa, jami'an tsaron kan iyakar kasar sun kashe daruruwan bakin haure daga kasar, kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen kasar ta sanar a ranar Talata.

Hukumomin Saudiyya ba su amsa bukatar jin ta bakinsu game da binciken ba. Wani jami'in Saudiyya ya fada a ranar Litinin cewa, zargin da ake yi a cikin rahoton da kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch (HRW) ta buga ba shi da tushe.

Sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Saudiyya ta fitar ta ce, "Gwamnatin Habasha za ta gaggauta gudanar da bincike kan lamarin tare da mahukuntan Saudiyya."

Sanarwar ta ce "a kauce wa yin jita-jita har sai an kammala bincike."

A wani rahoto mai shafuka 73 da ta fitar jiya Litinin, kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta zargi jami’an tsaron Saudiyya da aka jibge a kan iyakar Yaman da kai hare-hare kan ‘yan ci-rani, wadanda ke ketare kan iyaka da kafa.

HRW ta ce masu gadin sun yi amfani da bama-bamai wajen kashe wasu bakin haure tare da harbin wasu daga nesa.

Hukumar Tarayyar Turai ta bayyana cewa, za ta gabatar da sakamakon rahoton ga gwamnatin Saudiyya da mahukuntan Houthi na kasar Yemen.

Kakakin hukumar Peter Stano ya shaidawa taron manema labarai na yau da kullun cewa "Muna maraba da sanarwar da gwamnatin Habasha ta bayar musamman na yin bincike kan lamarin tare da mahukunta a Saudiyya."

Gwamnatin Amurka da Majalisar Dinkin Duniya sun kuma yi kira da a gudanar da cikakken bincike. A shekarar 2022 Jami’an Majalisar Dinkin Duniya sun yi zargin cewa, jami’an tsaron kan iyakar Saudiyya sun kashe bakin haure a bara, zargin da mahukuntan Saudiyyar suka musanta.

Hanyar ƙaura daga Habasha, ta ratsa mashigin tekun Aden, ta Yaman zuwa cikin Saudi Arabiya - ɗaya daga cikin ƙasashe mafiya arziki a cikin kasashen Larabawa.

~ Rueters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG