Shugaba Joe Biden ya yi marhabin da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da kungiyar Hezbullah, sai dai ana ci gaba da fafatawa a Gaza; Yayin da al'ummar Ghana ke shirin zaben shugaban kasa 7 ga watan Disamba, rundunar 'yan sandan kasar ta jaddada aniyar tabbatar da tsaro, da wasu rahotanni
Zababben Shugaban Amurka Donald Trump ya sha alwashin yin amfani da sojojin kasar wajen tasa keyar miliyoyin bakin hauren dake zaune a kasar ba tare da cikakkun takardu ba, shirin da ya sabawa al’adar Amurka ta yin amfani da sojoji a cikin gida
Kasar Isra’ila da kungiyar Hezbullah mai samun goyon bayan Iran na daf da kulla yarjejeniyar tsagaita wuta a yau Talata, abinda zai share hanyar kawo karshen rikicin da ya yi sanadiyar salwantar rayukan dubban jama’a tun bayan da yakin Gaza ya tayar da shi watanni 14 da suka gabata
Annobar COVID ta sauya duniya, a cewar sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, a jawabin daya gabatar a taron bunkasa tattalin arzikin kasashen Asiya da Pacific (APEC), na shekara-shekara dake gudana a birnin Lima, na kasar Peru.
Domin Kari