Shugaba Volodymyr Zelenskiy na fatan tattaunawar da za a yi a Jeddah za ta farfado da alakar Amurka mai “ma’ana” bayan ganawar da ya yi da Shugaban Amurka Donald Trump a watan da ya gabata wanda ya ba da shawarar cimma matsaya da Rasha a kan hanyoyin sama da kuma na teku.
Shawarar dai na da nufin nuna cewa yana kokarin cimma manufar Trump na kawo karshen yakin cikin sauri, bayan da shugaban na Amurka ya zargi shugaban Ukraine da rashin shirin neman zaman lafiya, ya kuma ci gaba da tattaunawa kai tsaye da Rasha.
Amurka, wadda ta ke babbar kawar Kyiv tun bayan mamayewar 2022, ta inganta manufofinta kan yakin tare da yin matsin lamba kan Ukraine, ta kuma dakatar da taimakon soja tare da dakatar da musayar bayanan sirri da Kyiv.
"Muna fatan samun sakamako mai amfani," in ji Zelenskiy gabanin tattaunawar a cikin wani sakon da ya kafa kan X a ranar Litinin. "Matsayin Ukraine a cikin wadannan tattaunawa zai kasance wanda zai samar da mafita."
A cikin daren ne Ukraine ta kai wani hari mafi girma kan birnin Moscow tund aka fara yakin, inda ta tura jiragen sama marasa matuka a kalla 91, suka kashe akalla mutum daya, da tada wuta, da rufe filayen tashi da saukar jiragen sama, da kuma tilasta karkatar da jiragen sama da dama, in ji jami'an Rasha.
Lokacin da aka kai harin wanda aka harbo jirage marasa matukai 337 a kan Rasha, a cewar Moscow, da alama an yi ne da nufin nuna cewa, har yanzu Kyiv na iya kai manyan hare-hare, bayan hare-haren makamai masu linzami na Rasha, wanda daya daga cikinsu ya kashe akalla mutane 14 a ranar Asabar.
Dandalin Mu Tattauna