Ci gaban da Rasha ta samu a gaba a 'yan watannin nan da kuma yunkurin Shugaban Amurka Donald Trump na cimma yarjejeniyar zaman lafiya don kawo karshen rikicin da aka kwashe shekaru uku ana yi a Ukraine ya haifar da fargabar cewa, Kyiv da ke samun goyon bayan kasashen Yamma za ta iya yin rashin nasara a yakin.
Wakilin Trump na musamman a Gabas ta Tsakiya Steve Witkoff ya isa Moscow yau Alhamis don ganawa da Putin. Jami'an Rasha sun ce mai ba Amurka shawara kan harkokin tsaro Mike Waltz ya ba da cikakken bayani kan ra'ayin tsagaita bude wuta jiya Laraba kuma Rasha a shirye take ta tattauna batun.
Yuri Ushakov, tsohon jakada a Washington wanda ke magana da Putin kan manyan batutuwan ketare, ya shaidawa gidan talabijin na kasar cewa ya yi magana da Waltz jiya Laraba don bayyana matsayin Rasha kan tsagaita bude wuta.
"Na bayyana matsayinmu cewa, wannan ba komai bane illa neman jinkiri na wucin gadi ga sojojin Ukraine, ba wani abu bane," in ji Ushakov.
Daga baya ya kara da cewa, "Hakan bai ba mu komai ba. Yana ba wa 'yan Ukraine damar sake hada kai, samun karfi da kuma ci gaba da abu daya."
Ushakov said Moscow's goal was "a long-term peaceful settlement that takes into account the legitimate interests of our country and our well-known concerns."
Ushakov ya ce manufar Moscow ita ce "tsakanin zaman lafiya na dogon lokaci wanda ya yi la'akari da halalcin muradun kasarmu da kuma abubuwan da suka dame mu da kowa ya sani."
Dandalin Mu Tattauna