Rukunin ministocin kasashe bakwai daga Birtaniya, Canada, Faransa, Jamus, Italiya, Japan da Amurka, tare da EU, zasu gana tsawon kwanaki biyu a garin La Malbaie da ake zuwa yawon bude ido, wanda ke kan tsaunin Quebec, a baya dai kasashen galibi sukan amincewa kan batutuwan da suka shafesu ba tare da wata jayayya ba.
Abin da ke kan gaba a jerin abubuwan da abokan huldar na Washington zasu tattauna, shine samun karin bayani kan tattaunawar da sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya yi da Kyiv a birnin Jeddah na kasar Saudiyya ranar Talata, inda Ukraine ta ce a shirye ta ke ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a yakinta da Rasha tsawon kwanaki 30.
Amma gabanin taron kungiyar manyan kasashen G7 na farko a karkashin jagorancin Canada, rubuta sanarwa karshe wadda dukkan kasashen suka amince da ita, ta kuma kunshi dukkan muhimman batutuwa ya kasance da wahala.
Matakin da Amurka ta dauka na sanya harajin kashi 25% kan duk karafa da dalma da ake shigar da su kasar sun sa ba tare da bata lokaci ba Canada da kasashen EU sanya harajin ramuwar gayya, abin da ya bayyana zafin takaddamar da ke tsakanin kasashen.
Dandalin Mu Tattauna