Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Kashe Dogo Saleh A Kokarin Ceto - ‘Yan sanda


Josephine Ade, kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Najeriya
Josephine Ade, kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Najeriya

Wani fitaccen shugaban ‘yan bindiga Salisu Mohammed, wanda aka fi sani da Dogo Saleh, mai shekaru 21, ya gamu da ajalinsa a hannun ‘yan kungiyarsa bayan da jami’an rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja suka kama shi.

Dogo Saleh, wanda aka bayyana a matsayin kasurgumin jagoran masu aikata miyagun laifuka da ke aiki a dajin Rijana na jihar Kaduna, ya kasance yana da alhakin yin garkuwa da mutane da dama a hanyar Kaduna zuwa Lokoja da zuwa Enugu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh, ta fitar da wata sanarwa a yau Larabar, inda ta bayyana cewa ‘yan sandan da ke aiki da bayanan sirri sun gudanar da wani samame a boye inda suka cafke Dogo Saleh a dajin Gidan Abe a ranar 3 ga watan Maris, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa karamar hukumar Bwari ta babban birnin tarayya.

Ta kara da cewa, bayan tattara bayanai daga wanda ake zargin, sashin yaki da garkuwa da mutane na rundunar ‘yan sandan ya kaddamar da wani samame a ranar 4 ga Maris, 2025, a wata maboyar ‘yan bindiga da ke dajin Kwasau, cikin karamar hukumar Kagarko, jihar Kaduna, inda ’yan kungiyarsa, karkashin jagorancin wani Abdu Musa, wanda ake kira da “Kanabaro,” suka kafa wata babbar maboya.

Ta lura cewa ‘yan bindiga sun yi wa jami’an kwanton bauna ne a kokarin kubutar da shugaban na su.

“Jami'an tsaron sun yi gaggawar afkawa tsundun cikin wani mummunan fada da ‘yan bindiga, tare da nuna kwarewa da juriya. Daga karshe dai an ci karfin ‘yan bindigar inda aka tilasta musu tserewa zuwa cikin dajin da munanan raunukan harbin bindiga. Dogo Saleh ya samu munanan raunukan harbin bindiga da ‘yan kungiyar sa suka yi masa a lokacin da suke musayar wuta. An garzaya da shi babban asibitin Kubwa, inda aka tabbatar da rasuwarsa,” in ji Adeh.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG