Shugabar hukumar tarayyar Turai Ursula Von der Leyen da Shugaban Majalisar tarayyar Turai António Costa, za su gana da Ramaphosa a ofishinsa da ke Cape Town a taron EU da Afirka ta Kudu na farko da za su yi tun shekarar 2018.
Kungiyar kasashen mai mambobi 27 za ta karkatar da hankalinta ne kan babbar kasar da take huldar kasuwanci da ita a yankin kudu da hamadar Sahara, bayan da kungiyar EU ta sanar da kakaba haraji kan Washington a matsayin martani kan sabon harajin da shugaban Amurka Donald Trump ya sanya kan karahuna da dalma da kasashen ke kaiwa Amurka.
Taron da za a yi a Afirka ta Kudu zai "duba sabbin hanyoyin hadin gwiwa a fannin tattalin arziki, kasuwanci da zuba jari, da kuma tattauna duk wani kalubale ko takaddamar cinikayya da ke tsakanin kasashen," in ji majalisar zartarwa EU.
Gwamnatin Trump dai ta sanya wa Afrika ta kudu takunkumi saboda wasu manufofin cikin gida da na waje da shugaban na Amurka ya bayyana a matsayin wadanda basu je daidai da muradan Amurka ba.
A watan da ya gabata ne Trump ya ba da umarnin dakatar da duk wasu kudade da Amurka ke ba Afirka ta kudu, inda ya zargi kasar da take hakkokin bil'adama akan farar fata tsiraru a kasar, da kuma goyon bayan wasu "miyagu" a duniya, kamar kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas da kuma Iran.
Dandalin Mu Tattauna