Geir Pedersen ya yi wannan kiran ne a ranar Juma’a, ranar da ake cika shekaru 14 da fara zanga-zangar neman demokradiyya wadda ta kai fiye da shekaru goma ana yakin basasa.
"Abin da ya fara a matsayin neman sake yin garambawul a harkokin mulkin kasar, ya gamu da mummunan zalunci, wanda ya haifar da daya daga cikin rikice-rikice mafyai muni a tarihin wannan zamanin," in ji Pederson.
“Rikicin ya fallasa mafi munin zaluncin ‘dan Adam. Iyalai na ci gaba da nuna alhinin rashin 'yan uwansu, al'ummomi na ci gaba da wargajewa, miliyoyin mutane sun bar gidajensu, kuma da yawa suna ci gaba da neman wadanda suka bata."
Majalisar Dinkin Duniya ta ce rikicin ya raba mutane kusan miliyan 12 da muhallansu a Syria, ciki har da 'yan gudun hijira sama da miliyan 6.
An hambarar da gwamnatin Assad ne a watan Disamban 2024, amma kazamin tashin hankali da aka fara a ranar 6 ga watan Maris a yankin gabar tekun Syria da ya janyo asarar rayuka, ya dakushe fatan samun kwanciyar hankali, inda jami’an tsaro suka yi artabu da mayakan da ke biyayya ga tsohon shugaban, wanda ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane, ciki har da fararen hula da dama.
Dandalin Mu Tattauna