Hukumomin jamhuriyar Nijer sun garkame tsohon Firaminista Hama Amadou a kurkukun Filingue da ke a tazarar km 198 a arewa maso gabashin birnin Yamai a bisa zarginsa da aikata wasu tarin laifuka sama da goma, matakin da magoya bayansa ke cewa bita da kullin siyasa ne.
A yau Asabar shugaban Amurka Joe Biden ya gabatar da jawabi a kan shirinsa na dala triliyan daya da biliyan 900 na tallafin COVID-19 da majalisar wakilai ta tabbatar da shi da safiyar yau.
Al'umar kasar Nijar tana kada kuri’a a yau Lahadi a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa wanda ake sa ran zai zama karon farko da gwamnatin farar hula zata mika ma wata sabuwar gwamnati ta farar hula a kasar da ke Afrika ta Yamma da ta samu ‘yancin kai daga Faransa a shekarar 1960.
Wani dan kwangilar tsaro mai zaman kansa kuma na hannun daman tsohon shugaban Amurka Donald Trump Erik Prince ya take dokar Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta haramta shiga da makamai a Libya, da masu binciken MDD suka gano da kuma kafafen yada labaran Amurka suka yada jiya Juma’a.
Amurka ta sake komawa cikin yarjejeniyar Paris a hukumance bayan da gwamnatin Trump ta fice daga yarjejeniyar ta sauyin yanayi, tana mai cewa shirin ya yi matukar tsada ba zata yi aiki da shi ba.
Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai da malaman su dake zaune a gidajen ma’aikatan makarantar gwamnati ta kimiya dake garin Kagara a jihar Neja.
Fitacciyar 'yar fim a Amurka Jada Pinkett Smith tare da kamfanin Westbrook Studio na Will Smith, zasu yi hadin gwiwa da wani shahararren kamfanin shirya fina finai a Najeriya na EbonyLife Studios, kan yin aiki tare wurin fitar da fina finai da shirye shiryen telbijin masu alaka da nahiyar Afrika.
Wani hadarin tarihi na lokacin sanyi da ya kara tsananin sanyi a akalla rabin fadin Amurka, ya sa sama da mutum miliyan biyu da rabi a Texas sun rasa wutar lantarki.
Masana sha’anin tattalin arziki da kungiyoyin kare hakkin mata a jamhuriyar Nijer sun yi na’am da matakin jaddada tsohuwar ministar kudin Najeriya Dr. Ngozi Okonjo Iweala a matsayin sabuwar shugabar hukumar cinikiyya ta duniya.
A jiya Asabar ministan kiwon lafiyar kasar Guinea ya ce mutum hudu sun mutu da cutar Ebola a wani sake bullar farko da cutar ta yi a cikin shekaru biyar.
Ajiya da marace ne wasu da ake zaton mayakan Boko Haram ne suka kai hari garin Gaidam dake jihar Yobe shiyar arewa maso gabashin Nageriya, sai dai al'umman garin Gaidam suka ce maharan basu sha da dadi ba a wajan jami'an tsaro ganin yadda aka fattatake su, wasu maharan sun arce da arsahin bundiga.
Majalisar dattawan Amurka ta kada kuri’ar bada sammacin gayyato shaidu su bada bahasi a wannan shari’ar tsige tsohon shugaban kasa Donald Trump.
Majalisar dattawan Amurka ta ci gaba da zama da safiyar yau Asabar a matsayin kotu a kan batun tsige tsohon shugaban kasa Donald Trump.
Afirka ta Kudu za ta fara yiwa ma’iakatan lafiya allurar rigafi da allurar rigakafin coronavirus da ba amince da ita ba da kamfanin harhada magunguna na Johnson & Johnson a mako mai zuwa, don ganin ko tana hana kamuwa da sabon nau’in cutar da ya bulla a kasar.
Hukumar zaben jamhuriyar Nijer na ci gaba da tuntubar rukunonin al’umar kasar da nufin tattara shawarwarin da zasu bada damar gudanar da zaben shugaban kasa na ranar 21 ga watan Faburairu cikin kyaukyawan yanayi.
Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta gargadi masu shirin sake gudanar da zanga zangar ENDSARS a Legas da su shiga taitayin su, bayan da wasu suka yi barazanar sake shiga zanga zangar da ta haifar da cece-ku-ce a baya a kan yanda ‘yan sanda suka yi amfani da karfin tuwo kan masu zanga zangar.
Wata shararriyar mawakiyar Amurka Mary Wilson da tayi fice a cikin fitattun mata mawaka uku da ake kira da The Supremes a cikin shekarun 1960 ta mutu tana da shekaru 76.
A yau Talata kasar Peru ta fara yaki da annobar coronavirus ta biyu da ta sake kunno kai, inda shugaban kasar Francisco Sagasti ya bayyana cewa allurar rigakafin bata da illa.
Hukumomi sun ci gaba da tsare Jimmy Lai, wani hamshakin dan kasuwa mai harkokin sadarwa kuma dan rajin dimokaradiya a Hong Kongbayan da babbar kotun yanki ta hana bada belinshi yayin da ya bayyana gaban ta yau Talata.
Dubban mutane sun fito a fadin Myanmar a yau Lahadi domin bayyana rashin amincewar su ga juyin mulkin makon jiya da kuma neman sakin zababbiyar shugaba Aung Sang Suu Kyi, a wata zanga zanagr da ba a taba ganin ba tun bayan juyin juya hali a shekarar 2007 da ya taimakawa sauyin dimokaradiyar kasar.
Domin Kari