Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta sake Komawa Cikin Yarjejeniyar Sauyin Yanayi A Hukumance


Shugaba Biden
Shugaba Biden

Amurka ta sake komawa cikin yarjejeniyar Paris a hukumance bayan da gwamnatin Trump ta fice daga yarjejeniyar ta sauyin yanayi, tana mai cewa shirin ya yi matukar tsada ba zata yi aiki da shi ba.

Fadar White House ta ce mummunar yanayi ta yi sanadiyar mutuwar mutum akalla 47 a jihar Texas da wasu jihohin Amurka a wannan mako, duka wani mummunar al’amari ne da sauyin yanayi ke haifar dashi.

Wasu iyalai da suka rasa wutar lantarki da ruwa sun nemi mafaka a wani shagon sayar da kayan kujeru da matsugunai da gwamnati ta yi tanadin su. Shugaban Joe Biden ya ce Amurka ba zata ci gaba da bata lokaci wurin shiga cikin yaki da sauyin yanayi ba.

A wani buki na sake shigar Amurka cikin wannan yarjejeniya, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce wannan mataki zai karfafa kokarin duniya a tinakarar batun dumamar yanayi dake tafiyar hawainiya.

Masana sun ce nada tsohon sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry a matsayin wakilin shugaban na farko a kan batun sauyin yanayi yana nuni da muhamminci da aka baiwa batun. Kerry ya yi alkawarin cewa Amurka zata ninka kokarinta.

Ya ce “mun sake komawa cikin wannan batun sauyin yanayin kasa da kasa da tawali’anci da buri. Tawali’u saboda mun yi asarar shekaru hudu da Amurka ta janye daga shirin, amma kuma burin shine yarjejeniyar ta Paris kadai ba zata iya yin abin da kimiya ta nuna mana mu yi tare.”

XS
SM
MD
LG