Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba Da Kada Kuri'ar Zaben Sabon Shugaban Kasa A Jamhuriyar Nijar


Mai kada kuri'a a Nijar
Mai kada kuri'a a Nijar

Al'umar kasar Nijar tana kada kuri’a a yau Lahadi a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa wanda ake sa ran zai zama karon farko da gwamnatin farar hula zata mika ma wata sabuwar gwamnati ta farar hula a kasar da ke Afrika ta Yamma da ta samu ‘yancin kai daga Faransa a shekarar 1960.

Dan takarar jami’iyya mai mulki Mohamed Bazoum ne ake ganin mutane da dama ke ra’ayinsa, bayan da ya tserewa abokan karawarsa a zagayen farkon a ranar 27 ga watan Disamba bara, inda ya samu kashi 39.3 cikin dari na kuru’un.

Yanzu yana karawa ne da tsohon shugaban kasa Mahamane Ousmane, wanda ya samu kashi 17 cikin dari.

Bazoum da ya rike mukamai da dama a gwamnatin dake barin gado ta shugaba Mahamadou Issoufou, ciki har da ministan harkokin kasashen waje da ministan cikin gida, yana samun goyon bayan ‘yan takarar da suka zo na uku da na hudu a zagayen farko na zaben.

Bazoum Mohamed
Bazoum Mohamed

A babban birnin kasar Yamai, an ga taron jama’a masu zabe, sanye da abin rufe fuska domin kariya ga COVID-19, suna cikin layuka a harabar makarantu cikin kura zasu kada kuru'un su.

Bazoum mai shekaru 61 ya lashi takobin ci gaba da manufofin shugaba Issoufou, na maida hankali kan batun tsaro, yayin da kasar ke fama da ayyukan ‘yan ta’adda, inda zai kuma fitar da wasu shirye shiryen farfado da tattakin arzikin kasar.

Mahamman Ousman
Mahamman Ousman

Shi kuwa Mahamane Ousmane mai shekaru 71 a duniya, shine shugaban farar hula na farko da aka zabe shi a Nijar kana sojoji suka hambarar da gwamnatinsa a shekarar 1996.

Shima ya samu goyon bayan kananan jami’iyyu a zagayen fako. Yayi alkawarin kawo sauyi da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

Kasar ta yankin Sahel mai mutum kimanin miliyan 24 kuma daya daga cikin kasashe matalauta a duniya da take kuma fama matsalolin fari da ambaliya.

Annobar coronavirus ta kassara tattalin arzikin kasar, yayin da faduwar farashin uranium da kasar ke aikawa waje, ya yi mummunar tasiri a kan kudaden shiga na kasar.

Hukumar lamuni ta kasa da kasa ta IMF tana sa ran tattalin arzikin Nijar zai sake farfadowa bayan annoba, da kashi shida cikin dari a wannan shekara bayan da ta yi kasa da kashi 1.2 cikin dari a shekarar 2020.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG