Tun bayan da kwamiti da gwamnatin jihar Legas ta kafa ya bada umarnin sake bude sansani da ake karban kuddaden motoci da suke wucewa da aka fi sani da “Lekki Toll Gate”, wasu suka bayyana rashin jin dadin su game da wannan matakin inda kuma suka shiga kafofin sadarwar zamani suka kira da a sake yin wani gangami.
Wasu kungiyoyi na daban suma sun shiga kafafen sadarwar zamani suka yi kira ga matasan dake neman sake yin zanga zangar da su shiga taitayin su, tare da kira ga Nnamdi Kanu jagoran kungiyar neman ‘yancin ‘yan kabilar Ibo da cewa shima ya shiga taitayin sa.
Wasu mazauna Legas da suka tattauna da Sashen Hausa sun bayyana rashin jin dadin su a kan yadda gwamnatin jihar ta gaza wurin fitar da alkalumma a kan wadanda suka shirya wannan abu a cikin gida da waje domin a hukunta su kowa ya gani ba.
Mutum na farko da ya tattauna da wakilin mu a Legas ya ce “in har gwamnati ta zuba ido ta kyale ana shirya irin wannan abu daga kasashen waje kuma a aiwatar a cikin gida ba tare da daukar wani kwakkwaran mataki ba, toh yaushe kasar zata yi hukunci da zai zama izina ga saura.”
A cewar wani kuma da ya tattauna da wakilin mu, manufar masu zanga zangar ce su wargaza gwamnati baki daya, saboda da an zauna aka zuba musu ido zasu cimma manufar su, don sun fada cewa zasu fadada zanga zangar zuwa duk fadin Najeriya amma al’ummar arewa su gane suka kuma ki basu hadin kai. Ya ce duk tanadi da suke yi ya kusan zuwa karshe kana ba zasu yi nasarar wargaza kasar ba.
Wasu mambobi hudu a kwamitin da aka kafa su ma sun bayyana rashin amincewar su da umarni da shugabar kwamitin ta bayar na sake bude wannan sansani na karban kudade shiga na motocin dake bi wannan shataletale na Lekki, abin da kuma ya kawo rarraba kawuna tsakanin ‘yan kwamitin da gwamnatin jihar ta Legas ta kafa domin gudanar da bincike a kan waccan hargitsi da aka ce ya yi sanadiya mutuwar wasu masu zanga zanga sakamakon zargin bude wuta kan masu zanga zangar da ake yiwa sojoji da aikatawa.
Ga rahoton da wakilin mu Babangida Jibrin ya aiko mana daga Legas: