Remy Lamah ya fadawa kamfanin dillancin labaran AFP cewa "muna matukar damuwa game da wadannan mace mace na farko tun bayan barkewar annobar daga 2013 zuwa 2016 a Guinea da ta hallaka mutum 11,300 a fadin yankin."
Daya a cikin sababbin mutanen da suka harbu da cutar itace wata ma’aikaciyar nes da ta yi ciwo a karshen wata Janairu kana aka bisa ta a ranar farko ga watan Faburairu, a cewar shugaban hukumar kiwon lafiya Sakoba Keita yana fadawa kafar yada labarai ta cikin gida.
Ya ce a cikin wadanda suka je bison, mutum takwas sun nuna alamun harbuwa, inda suka fara zawayi da amai da kuma zubar da jinni.
Mutum hudu da suka mutu da cutar Ebolar suna zaune ne a Nzerekore dake kudu maso gabashin kasar, inji Keita.
Keita ya kuma fadawa kafafen labaran cikin gida cewa wani mara lafiya ya arce amma dai an kama shi har an kwantar da shi asibiti a Conakry babban birnin kasar. Ya kuma tabbatarwa AFP batun amma bai yi wani karin bayani ba.
Hukumar kiwon lafiya ta duniya, WHO, ta kalli sake barkewar cutar tun cikin shekarar 2016 a cikin matukar damuwa kana tana daukar labarin gano cutar da aka yi a kwanan nan a kasar Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo a matsayin kalubalen kiwon lafiya na kasa da kasa.