Hama Amadou wanda shi da kansa ya gabatar da kansa a ofishin ‘yan sandan farin kaya a ranar Juma’ar da ta gabata bayan da ya samu labarin hukumomin na nemansa ruwa a jallo, ya gurfana a gaban alkali mai kare muradun gwamnati da yammacin jiya Litinin inda aka karanta masa wasu laifuka sama da a goma da ake zarginsa da aikatawa kafin wucewa da shi gidan yarin Filingue. Lauyansa Me Mossi Boubacar ya yi wa Sashen Faranci na Muryar Amurka karin bayani.
Ya ce “wasu jerin laifuka ne ake zargin ya aikata cikinsu har da hada kai da wata kungiyar da ke yunkurin kawar da halaltacciyar gwamnati da kafa kungiyar ‘yan ta-kife, sai zargin tunzura jama’a da zargin furta kalaman kabilanci da dai sauransu. Abin ba kan gado.”
Magoya bayan Hama Amadou sun yi tir da wannan mataki koda yake a cewarsu ba su yi mamaki ba domin a tunaninsu tsararriyar ajanda ce aka soma zartarwa da zummar cimma wata manufar siyasa.
Alhaji Mahamadou Maidouka na daga cikin kusoshin jam’iyyar Moden Lumana ta Hama Amadou, ya kuma tattauna da Sashen Hausa a kan wannan batu.
Wasu daga cikin shugabannin ‘yan hamayyar da suka bakwanci gidan yari a jiya saboda zarginsu da hannu a zanga zangar watsi da sakamakon zagaye na biyu na zaben shugaban kasar sun hada da tsohon kwamandan rundunar mayakan Nijer Gen. Moumouni Boureima da aka kai gidan kason Ouallam yayin da aka ajiye Abdou Maman Lokoko na jam’iyar Muna Tare da Tahirou Seidou Maiyaki na Moden Lumana a gidan yarin Say yayin da a Damagaram hukumomi ke ci gaba da tsare Abdoulrahim Balarabe na jam’iyar RDR Canji da wasu kusoshin jam’iyyun hamayya.
Tuni ‘yan rajin kare hakkin jama’a irinsu shugaban kungiyar CADDED, Dambaji Son Allah suka fara jan hankula a kan maganar mutunta ‘yancin wadannan ‘yan siyasa.
Da ma tun a tsakiyar watan jiya alkali mai kare muradun hukuma ya sanar cewa ya na bin diddigin abubuwan da ke faruwa a yakin zaben da ya gabata wanda a cewarsa ya lura da wasu ‘yan siyasa na amfani da kalaman da ba su dace ba, sannan ya ce muddin wasu abubuwa na hargitsi suka biyo bayan wadannan jawabai zai dauki matakin hukunci a kan irin wadannan ‘yan siyasa, sai dai ‘yan hamayya na ganin an sa son rai wajen zartar da wannan kudiri.
Wakilin Muryar Amurka a Yamai Souley Moumouni Barma ya aiko mana Karin bayani: