Peru ta fara bada zagayen farko na rigakafin wuni biyu kacal bayan da ta samu zubin rigakafin dubu dari uku daga dakin gwaji na Sinopharm na kasar China.
Mai Magana da yawun ma’aikatar kiwon lafiyar Peru, tace hukumomi suna sa ran alluarar rigakafin zata maido da kwarin gwiwa na tinkarar wannan annoba.
Ministar kiwon lafiya Pilar Mazzetti, ta jinkirta karban rigakafin, tana jira ma’aikatan kiwon lafiya dake yaki da cutar su fara samu tukuna.
Peru, da take cikin kasashen masu yawan wadanda suka kamu da coronavirus a yankin Latin America, ta tabbatar da mutum miliyan guda da dubu 186 suka kamu kana wasu dubu 42 da 308 suka mutu da cutar, a cewar cibiyar sa ido a kan cutar ta Jami’ar John Hopkins.